Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya karyata zargin da abin da ya kira ji-ta-ji-tar da ake watsawa a soshiyal midiya cewa ya fara yi wa Yankin Kudu maso Yamma kamfen din karbar shugabancin kasar nan a 2013.
Wani bayani da aka rika watsawa da sunan Lawan, ya nuna ya na goyon bayan a bai wa yankin Kudu Maso Yamma mulki a 2023, domin a karrama marigayi Mashood Abiola.
An ce Lawan ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC su damka mulki ko takarar shugaban kasa ga dan yankin Kudu maso Yamma a 2023.
Sai dai kuma Sanata Lawan ya musanta wannan labari da ke yawo.
Ya ce an yi furucin, amma ba shi ne ya yi ba, wani mai irin sunan sa ne, kuma Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Adamawa.
Lawan ya musanta wannan furuci ne yau Litinin a shafin san a Twitter mai suna @DrAhmadLawan.
“ An jawo hankali na game da wani furuci da ke yawo a kafafen yada labarai, inda aka ce na ce tilas a mika mulki ga Shiyyar Kudu maso Yamma a 2023. Wannan ba haka ba ne, ba ni ne na yi wannan magana ba.
“Wannan kalami Sakataren Jam’iyyar APC na jihar Adamawa ne, wanda sunan mu daya, shi ma sunan sa Ahmed Lawan, ya yi furucin. “Saboda haka jama’a su tantance.
Discussion about this post