Kashi 20 bisa 100 masu koyarwa a Bauchi duk malaman bogi ne –Gwamna

0

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya bayyana cewa kashi 20 bisa 100 na malaman da ke koyarwa a Jihar Bauchi, duk dodorido ne, babu su, na bogi ne.

Gwamna Bala ya ce abin bakin ciki kuma wadannan sunayen na bogi duk ana yin amfani da su a duk karshen wata ana kwasar albashi.

Bala ya yi wannan fallasa ce a Bauchi jiya Lahadi a lokacin da ya ke wa matasa jawabi domin tunawa da Ranar Kananan Yaran Afrika ta Duniya.

Gwamnan ya ce gwamnatin da ta shude ta rika daukar ajingizon ma’aikatan bogi, alhali ga dimbin malamai nan birjik da suka yi aikin horon koyarwa su na zaune babu aiki.

Bala ya ce gwamnatin sa za ta bi diddigin yawan malamai da kuma gano makudan kudaden da suka salwanta a fannin biyan malaman albashi.

Sannan kuma ya ce zai binciki kwangilolin da gwamnatin da ta shude ta bayar.

Ya ce zai kaddamar da yaki a kan wadanda ya kira “wadanda ba su neman jihar Bauchi da alheri”, wadanda ya ce su ne suka maida jihar ta zama koma-baya.

Ya kara da cewa zai gurfanar da tsoffinn jami’an Hukumar Bayar Da Ilmi a Matakin Farko (SUBEB), saboda rawar da suka taka wajen tabargaza da makudan kudaden hukumar.

Daga nan sai ya nuna rashin jin dadin yadda makarantu da dama a fadin jihar duk iska ya kwaye rufin su, dalibai na karatu a karkashin inuwar bishiyoyi, duk kuwa da irin makudan kudaden da Hukumar SUBEB ta yi ikirarin ta kashe a fannin ilmi.

“Ni ban ma san aikin da gwamnatin da ta gabata ta ke yi ba da har ta bari gine-ginen makarantun jihar Bauchi suka yi mummunar lalacewa haka.” Inji Bala, wanda ya taba yin ministan babban birnin tarayya, Abuja.

Daga nan sai ya yi alkawarin cewa zai dauki wasu mata su 1000 aikin koyarwa, wadanda aka yi wa horon aikin malanta a bisa hadin guiwa da UNICEF.

Share.

game da Author