NBTS na bukatan ledan jini miliyan biyu duk shekara a Najeriya – Ma’aikatar kiwon lafiya

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa duk shekara dakunan adana jini ta kasa (NBTS) na bukatan ledan jini miliyan biyu domin ceto rayukan mutane a kasar nan.

Babban sakataren ma’aikatan kiwon lafiya Abdullahi Masah ya sanar da haka a taron wayar da kan mutane game da mahimmancin bada gudunmawar jini da aka yi a Abuja.

Masah ya ce mutane da dama musamman yara, mata da wadanda suka yi hadari sun rasa rayukan su a asibitocin kasar nan a dalilin rashin jini.

“ Hakan na da nasaba ne da rashin bada jini da mutanen kasar nan ke kin yi.

Ya ce domin kawar da wannan matsalar ma’aikatar su ta samar da ingantattun kayan aiki na zamani a duk cibiyoyin NBTS dake kasar domin inganta aiyukkan su.

Masah ya ce NBTS za ta sami nasara ne idan mutane sun mara wa NBTS baya ta hanyar bada gudunmawar jinin su.

Ya ce suna sa ran cewa haka zai taimaka wajen samar da ingantaciyyar jinin da ake bukata a kowani lokaci a kasan.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya koka kan yadda mutane ke kin bada gudunmawar jini da yake ta yawaita a kasar nan yanzu.

Adewole ya fadi haka ne bayan sun gano cewa NBTS na bukatan ledan jini akalla miliyan 1.8 domin ceto rayukan mutanen marasa lafiya a kasar nan.

Ya ce bada gudunmawar jini na taimakawa wurin ceto rayukan mutane musamman mata da yara kanana.

” Sai dai kuma kashi 10 bisa 100 ne na mutanen kasar nan ke bada gudunmawar jini kyauta, kashi 60 bisa 100 ko sai an biya su sannan kashi 30 su kan bada jini ne kawai idan wani na su na bukata.

Adewole ya ce maza za su iya bada gudunmawar jini bayan duk wata hudu sannan mata bayan wata uku.

Share.

game da Author