BADAKALAR MAKAMAN AMOSUN: Babu ruwan mu – Dasuki, Jonathan

0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonatahn ya bayyana cewa babu wani lokaci da gwamnatin sa ta ba tsohon gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun damar ajiye makamai a fadar gwamnati ko kuma ma ya shigo da su.

” Gwamnatin Jonathan bata taba amincewa tsohon gwamnan Ogun ya shigo da gwamnati. Ba ataba ba da wannan dama ba.” Wani minista da yake da iko a lokacin mulkin Jonathan ya bayyana wa PREMIUM TIMES.

Sai dai kuma ya shawarce jaridar da ta nemi ji daga bakin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki domin samun karin bayani.

PREMIUM TIMES, ta nemi ji daga bakin Dasuki duk da cewa yana daure, wani ma’aikacin ofishin a wancan lokaci ya bayyana cewa idan dai daga ofishin Dasuki ne, ba sai anyi tambaya ba, donin Dasuki bai taba ba wani gwamna lasisin shigo da makamai irin haka ba.

Idan ba a manta ba gwamnonin kasar nan sun maida wa tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun aniyar sa, bayan ya yi furucin cewa ai gwamnoni kan gina manyan rumbunan ajiyar makamai a Gidan Gwamnati.

Amosun ya yi wannan zargin ne a ranar Talata, a lokacin da ya ke kokarin sabule rigar alhakin boye tulin makamai a fadar Gidan Gwamnatin Jihar Ogun, wanda PREMIUM TIMES ta fallasa ya yi a lokacin da ya na gwamna.

Tulin makaman wadanda ya sayo da kudin gwamnati a asirce, kuma ya kimshe a asirce ba tare da sanin jami’an tsaro da sauran hukumomin tsaro ba, babban laifi ne, kuma karya dokar safarar makamai ce ta kara.

Manyan jami’an tsaro na Najeriya sun cika da mamakin yadda Amosun ya shigo da makaman ta haramtacciyar hanya da kuma tababar abin da aka yi niyyar yi da su.

Share.

game da Author