ZARGIN FYADE: Sharri ake min – Fasto Cocin COZA

0

Shugaban cocin ‘Common Wealth OF Zion Assembly COZA’ Abiodun Fatoyinbo ya mai da martini game da zargin yi wa ‘yar shekara 17 fyade da ya karade kafafen yada labarai.

Fatoyinbo ya musanta aikata haka inda ya bayyana cewa wannan yarinya wanda matar wani fitaccen mawaki ne Timi Dakolo mai suna Busola ta shirga masa karya ne cewa bai aikata hakan ba.

“Tun da nake ban taba yi wa wani ko wata fyade ba kuma na yi mamaki matuka game da abin da ta fada ganin irin kimar da mijinta wato Timi ke da shi a kasar nan.

“Tabas na san iyayen Busola domin a lokacin da na san su na fara aikin kafa coci na a Ilori kenan a 1999. Amma ban da addu’o’in da nake yi tare da iyalen ban taba zama ni kadai ba a wani wuri tare da Busola ”.

Fatoyinbo ya fadi haka ne a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranan Juma’a.

A ranar Juma’a ne Busola Dakolo ta bayyana cewa Fasto Fatoyinbo ya yi mata fyade a gidan iyayenta a lokacin da take shekara 17.

Busola ta fadi haka ne a hira da wakilin jaridar ‘YNaija’ Chude Jideonwo.

Busola ta ce Fasto Fatoyinbo kan zo gidan su ne yi wa iyayenta addu’a ” a nan ne fa wata rana da ya zo gidan mu da sassafe ina bude kofa kuwa ya turani kan kujera ya danne ni da karfin tsiya yayi lalata da ni.”

Ta ce shugabannin cocin da iyayenta duk sun san abinda ya faru tun a wancan lokaci. Tace ya rika rokonta ta yafe masa idan ya tuna abinda ya rika yi da ita.

Bayanai sun nuna cewa wannan ba shine karo na farko ba da ake zargin wannan fasto da aikata irin haka da mabiyan sa.

Fitattun mawaka irin su DON Jazzy,Toke Makinwa,Daddy Freeze sun sun jinjina wa Busola suna yaba mata bisa tona wa wannan fasto asiri da tayi.

Sai dai wani cikin masu taimakawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya ce bai ga alamun gaskiya ba game da zargin fyaden da Busola ta yi wa faston ba.

“Ni ba masoyin Fatoyinbo bane amma a ra’ayina kamata ya yi mu yi amfani da hankalin mu waje tantance maganar da ta yi.

“Dama shaidan kan yi amfani da mutane irin haka domin bata sunan masu aikin Allah irin haka. Idan ba sharri ba ta yaya za a ce bakon da bai da masaniya game da adaddin yawan mutane dake cikin gidan ka a wannan lokaci zai shigo gidan ka ya danye yarinyar ka a cikin sanyin safiya haka kawai? Mutane ku yi tunani mana!”

Share.

game da Author