Tsohon Ministan Harkokin Yada Labarai, Lai Mohammed, ya shiga tsomomuwar bayar da shaida a gaban mai shari’a, domin bayyana abin da ya sani dangane da badakalar naira biliyan 2.5 ta kwangilar da ake zargin Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Talabijin da Radiyo na Tarayya, Ishaq Modibbo ya tafka.
Hukumar ICPC ce da kan ta ta bayar da sanarwar cewa za ta gayyaci Lai gurfana a kotu domin bayar da shaida.
ICPC dai ita din ce ta gurfanar da Modibbo a kotu saboda zargin kulli-kurciya da aka yi da naira bilyan 2.5 na somin tabin wata kwangilar kafa na’urorin kara karfin tashoshin NTA.
An buga haka a shafin ta na intanet, sannan kuma ita ICPC din da kan ta a jiya Alhamis, ta kuma tabbatar da hakan ga PREMIUM TIMES, bayan ta buga a shafin ta intanet.
Sai dai kuma ta kara da cewa Lai Mohammed zai gurfana ne a matsayin mai bada shaida, ba wanda ake tuhuma da zargin sanin dukkan abin da ake kullawa ko aka rigaya aka kulla kafin da kuma bayan da aka karkatar da kudaden ba.
ICPC na cajin Kawu Modibbo, Lucky Omoluwa da Dapo Onifade Shugaban Kamfanin Pinnacle Communications Limited da zargin karkatar da kudaden.
An gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Folashade Ogunbanjo-Giwa.
Duk da dai ICPC da kuma shi kan sa Lai Mohammed sun jaddada cewa Ishaq Kawu din ne ya yaudari Lai amince ya sa wa kwangilar da biyan kudin kwangilar hannu a matsayin sa na Ministan Yada Labarai da ke sama da shi Shugaban Hukumar NBC din, hakan bai tserar da Lai daga zargin cewa da shi a cikin harkallar ba.
Wannan ikirari da Lai ya yi cewa ‘yar-burum-burum Shugaban NBC ya yi masa, shi ne kuma mai bayar da shaida na ICPC mai suna Osanato Olugbemi ya gabatar a gaban kotu.
Sai dai kuma an shaida wa kotu cewa yadda aka bayar da kwangilar da kuma irin baudadden tsarin da aka bi aka fitar da kudaden da kuma wadanda aka bai wa kudaden ko kuma aka ce an fitar wa kudaden da kamfanin na su, duk abin ya zo cikin hanyoyi na kumbiya-kumbiya.
An kara shaida wa kotu yadda Pinnacle Communication ya yi sauri a cikin gaggawa ya karkasa kudaden da aka ba shi, ya yi musu rabon-tuwon-gayya zuwa wurin mutane 47, jim kadan bayan shigar da kudaden cikin asusun ajiyar sa na banki.
Kafin a zo lokacin gayyatar Lai a kotu a yanzu, shugabannin kamfanin da shi kan sa Shugaban NBC sun sha kin amsa gayyatar kotu.
Sai da ta kai mai shari’a ya bada umarnin a kamo mata Ishaq Kawu ko da a kan gadon asibiti ya ke.
Za a ci gaba da sauraren karar a ranar 1 Ga Yuli, 2019.
Discussion about this post