Awoyi 24 bayan kashe mutane 18 da mahara suka yi a karamar hukumar Tsafe, an far wa garin Yankaba, dake Karamar Hukumar Kauran Namoda inda suka waske da Hakimin garin da matansa uku.
Kamar yadda shugaban karamar hukumar Kauran Namoda Lawal Isa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun farwa garin Yankaba da misalin 11:30pm na dare.
Ya ce ko da suka farwa kauye sun nufi gidan Hakimin garin Buhari Ammani.
Baya ga shi da aka yi garkuwa da maharan sun tafi da matansa uku masu suna Jummai, Asma’u da Lami sannan kuma da dan sa daya mai shekaru 13.
Bayan haka sun kashe Siddiki Abubakar wani dan garin sannan suka yi garkuwa da wani malami mai suna Aminu Nakano da wani Ismaila Isah.
Idan ba a manta ba gwamna Bello Matawalle ya roki maharan da su ajiye makaman su su runguma zaman lafiya.