Sama da shekara daya bayan shirin ajiyar kudade a karkashin Tsarin, Mavrodi Mundial Moneybox (MMM) ya kassara sama da mutane milyan uku, yanzu kuma an dawo da shirin ka’in-da-na’in.
Wannan sabon tsari, wato MMM, dillalan sa sun yi wa duk wanda ya yi shahadar-kuda ya ajiye kudade a asusun sa, to idan ya tashi karba za a kara masa kashi 50 bisa 100 na adadin kudaden da ya ajiye.
Ba kamar wannan tsari na farko da suka yi wanda ya rushe ba, inda ake bai wa mai ajiya karin kashi 20 bisa 100 na kudaden da ya ajiye kadai.
Kamar dai wancan tsarin na farko, duk mai son shiga MMM zai yi rajista, zai zuba wasu kudade a karkashin tsarin “taimakar ni, na taimake ka.” Za ka kwashi adashin kudade da ka zuba bayan kwana 30, tare da ribar da za a dora maka.
Kamar yadda suka fada a jiya Asabar a shafin su na intanet, sun ce sun fara tun ranar 22 Ga January, 2019.
“Mun dawo bayan watanni biyar da sake nazarin tsohon tsarin adashin mu. Yanzu MMM ya mamaye duk duniya tun daga 22 Ga Janairu, 2019.
Bayan abin da ya faru a wancan zubin adashi na baya, inda bayan tattara kudaden jama’a, shugaban tarin kudin Loom Ponzi ya mutu, ana tunanin ‘yan Najeriya sun koyi darasi. Amma abin mamaki za su sake afkawa rijiya gaba dubu.
Yayin da wasu ke ta kokarin neman shiga adashin, wasu kuma sun ki yarda su sake jefa kafar su a cikin tarkon da ya taba rike masu kafa a baya.
Mista Mavrodi, wanda shi ne mai MMM, ya rasu cikin 26 Ga Maris.
Dama kuma tsohon mai laifi ne da aka taba daurewa a kurkuku.
Tun cikin 2016 wannan tsarin adashi ya ruguje a cikin kasashe da dama, abin da ya janyo rikita-rikita.
An kirkiro adashin cikin 2011, amma kuma ya ruguje cikin 2016 a Najeriya, inda milyoyin kudaden mutane suka makale a cikin asusun ba tare da sun cire ba.