Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bada sanarwar cewa ta janye satifiket na shaidar nasarar zabe ga mutane 70, wadanda aka bayar bayan zaben 2019.
Kwamishinan Wayar da Kai na Kasa, Festus Okoye ne ya shaida haka a wani taron da Gidauniyar Kofi Annan ta shirya a Abuja.
Okoye ya kara da cewa daya daga cikin manyan kalubalen da INEC ke fuskanta, sun hada har da rigingimun zaben fidda-gwani da a kotuna tun kafin a yi zaben 2019.
‘‘Ya zuwa yau din nan INEC na da kararraki 809 wadanda ke kotu tun kafin a yi zaben 2019, sai kuma wasu 800 da aka kai kotuna bayan zaben 2019 din.
“Ya zuwa ranar Talata, INEC ta janye satifiket 70 daga wasu da a farko ta bayyana sun yi nasara a zabukan majalisar jihohi da ta tarayya.
“An kwace su ne bayan da kotu ta yanke hukuncin cewa ba su ba ne halastattun ‘yan takara, ko kuma ba su ba ne suka yi nasara. Kuma INEC ta sake buga wasu satifiket din, ta bai wa wadanda kotu ta ce su ne halastattu.
“Mu na kuma kara ci gaba da kwacewa da ci gaba da sake bayarwa ga wadanda kotu ta ce su ne halastattu.
“Da yawan wadannan sun faru ne sakamakon rashin adalcin da wasu jam’iyyu suka tafka a zabukan fidda-gwani. Wannan abu ya na damuwar mu, kuma har zuwa yau din nan akwai sauran shari’un rikta-riktar zabukan fidda-gwani a kotuna daban-daban.”