Yunkurin Cin Amana Da Butulcewa Masarautu A Arewa, Daga: Imam Murtadha Gusau

0

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Ya ku bayin Allah! A yau Allah ya kawo mu wani irin zamani da kusan sai dai muce Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’uun!

‘Yan uwana masu daraja, dalili kuwa shine, kamar yadda kuka sani, tun kafin kasar mu Najeriya ta samu ‘yancin kai Sarakunan mu masu girma, masu daraja sune suke kokarin dawainiya da al’ummah, domin sune suka fi kusa da Al’ummah, sune suka fi kusa da talakawa.

Wallahi duk wata Jaha da zaka tafi, musamman a Arewacin Najeriya, zaka tarar cewa Sarakuna sun bayar da gagarumar gudummawa marar misaltuwa wurin kafa wannan Jahar tare da kokarin samar da duk wani cigaba da ake tinkaho dashi a yau.

Hakanan idan kazo kan duk wasu Shugabanni da ‘yan siyasa da suka zama Shugabannin Al’ummah a yau, wallahi zaka tarar kusan Masarauta ce ta dauki nauyi ko kuma ta yi hanyar samar da Ingantaccen ilimi a gare su.

Amma duk da wannan, zaka tarar, abin bakin ciki, abin mamaki, kuma abin ban haushi, wai an wayi gari a yau, da sunan cigaban zamani na karya, babu inda wasu ‘yan siyasa a yanzu suke kokarin ci wa mutunci, da yiwa kazafi, sharri, kage, da karya, kamar Masarautar nan da tayi masu gata, ta taimaka wurin zaman su wani abu a rayuwa!

Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Ya ku bayin Allah! Ya ishe mu ishara, ya ishe mu nuni da abin da ya faru a Jahar Kano. Da yawan mu mun dauka cewa Masarautar Kano Masarauta ce da iya Kanawa kadai ke amfanuwa da ita. A’a wallahi ba haka bane. Masarautar Kano Masarauta ce da kusan duk fadin Najeriya kowa yana amfanuwa da ita ta hanyoyi daban-daban. Kuma wannan ko mun sani ko bamu sani ba. Sai dai kuma idan za muyi butulci ne da muka saba!

Ya ku jama’ah! Kwatsam, ba mu gama jimami da bakin cikin abinda ya faru a Kano ba, sai muka ji labarin wai shima Gwamnan Jahar Filato, Mista Simon Lalong yana son ya kwaikwayi takwaransa na Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wurin cin mutuncin Masarauta. Wannan yana nuna muna cewa kusan Gwamnonin Arewa kudurin da zasu fara karin kumallo da shi a Next Level, shine su ci mutuncin Masarauta.

Wannan yana ishara kenan zuwa ga cewa dukkanin wani Sarki mai kaunar talakawa tsakanin sa da Allah, wanda yake da jajircewa da kokari wurin fadin gaskiya, azzaluman ‘yan siyasa za su iya yi masa barazana da sauke shi ko kuma rage masa karfi kenan?

Yanzu kenan a yankin mu na Arewa an kai matsayin da talaka bashi da gata sai na Allah kenan?

Fa Inna lillahi wa inna ilaihi raji’uun!!!

Wallahi ya kamata talakawan Najeriya mu farka daga dogon baccin da muke yi, domin mu gane matsalar da ke gaban mu, kuma mu fahimci su waye suke kaunar mu tsakani da Allah kuma su waye makiyan mu!

Domin duk lalacewar uba sunan sa uba, uba yana kuma da ranar sa. Don haka Sarakunan mu wallahi sune iyayen al’ummah.

Ina fata, tare da rokon Allah ya cigaba da bamu Shugabanni nagari. Azzaluman Shugabanni kuwa, ya Allah ka shirya muna su, idan ba zasu shiryu ba kuwa, ya Allah ka yi muna maganin su.

Ya Allah ka ba mu wadanda za su so mu, wadanda za su ji tausayin mu, tare da kishin mu ba kishin kan su ba, amin.

Mai girma, marigayi Dan masanin Kano, Alhaji Maitama Sule, ya hakaito muna wani tarihi mai ban al’ajabi, wanda yake nuna irin yadda Gwamnan Kano Ganduje ya amfana da Masarauta, wadda a yau yake kokarin ci wa mutunci, don kawai son zuciya irin na siyasa. Ga tarihin kamar haka:

“Sarkin Ganduje Umaru, mahaifin Gwamna Ganduje, bawan Madakin Kano Ibrahim ne daga cikin bayin sa na Fulani. Sabo da soyayya da kaunar da take tsakanin su, ya yanka Dawaki, ya nada shi Dagacin Ganduje. Madakin Kano Bello kuma, wata rana Dagacin Ganduje yazo gaisuwa sai Madaki Bello ya tambaye shi: “Ina danka Abdullahi?” Sai Dagacin Ganduje yace: “Ya tafi kiwo.” Sai Madaki Bello yace: “Lallai gobe kar yaje kiwon. Ka kawo min shi na ganshi.” Da safe gari ya waye sai Dagacin Ganduje ya kawo dan sa wurin Madaki kamar yadda aka umarce shi. Madaki Bello yana fitowa sai yace: “Ina Headmaster?” Dauki yaron nan ka tafi dashi makaranta.” ~ Marigayi Dan Masanin Kano Maitama Sule

‘Yan uwa, kun ji yadda Ganduje da mahaifin sa suka mori Sarauta. Shi kuma ga sakayyar da yake so yayi mata a yau.

Ya ku bayin Allah! Sannan ku saurari karya da sharri da kazafi da wasu jaridu suka buga, domin wai a sa jama’a su ki jinin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, domin wai jama’ah suce ai shine ya janyo wa kan sa duk wannan abin da yake faruwa a kan sa. Kuma sun tsara wannan karyar ne saboda wai su rage wa Mai Martaba Sarki farin jinin da Allah yayi masa wurin jama’ah. Alhali sun manta da cewa, ba yin sa bane yin Allah ne. Ga abinda wai suke cewa kamar yadda jaridu suka ruwaito:

“Wata majiya dake da alaka da gwamnan Kano ta fada cewa wai sau biyar Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II yana ganawa da shugaban kungiyar Kwankwasiyya, kuma tsohon gwamnan Kano Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma dan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP, wato Abba Kabir Yusuf, wanda kuma wadannan ne manyan ‘yan adawar Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wai sun gana ne domin daukar matakan da duk suka kamata na ganin cewa PDP ta samu nasarar darewa kujerar gwamnan Kano. Sa’annan wata majiyar kuma ta daban ta bayyana cewa Sarki Sanusi ya umurci dukkanin dagatai da hakiman sa akan cewa lallai su tabbatar da jama’iyyar APC bata kai labari ba a zaben gwamnan da ya gabata, sannan kuma wai Sarki yayi amfani da kusancin sa da manya wajen tara kudade masu yawan gaske da wai jam’iyyar PDP za tayi amfani dasu a zabe domin tabbatar da samun nasarar ta. Suka ci gaba da cewa, wai Sarkin bai tsaya haka ba, a ranar da za ayi zabe, a ranar 23 ga watan Fabrairu, wai Sarki ya tara dukkanin jama’ar dake fadar Masarautar Kano, sannan ya umurce su da su zabi jama’iyyar PDP, wanda kuma wai hakan akayi, har ya kasance wai PDP ce taci akwatun dake gidan Sarki gaba daya, a sakamakon umurnin da wai Sarki bayar. Abin bai tsaya iya nan ba, wai hatta kuri’ar Sarkin ma an gano cewa PDP ya zaba, wai sabanin wani irin abu da tsohon Sarkin Kano Ado Bayero yake yi, na dukunkune kuri’ar sa in yayi zabe ya jefa akwatu ta yadda ba za’a taba gane me ya zaba ba. Baya ga nan wai an gano cewar Sarki ya umarci dagatai da masu unguwanni dasu gabatar da rahoton cewa akwai tashin hankali ga hukumomin tsaro a tsakanin zaben gwamna zagaye na farko da zagaye na biyu don ganin cewar wai ba’a gudanar da zaben a zagaye na biyu ba, inda wasu masu unguwannin suka ki bin wannan umarni. Baya ga nan wai Sarki ya taka rawa wajen gabatar da jawabai ta kafafen watsa labarai wadanda suke nuna cewar Gwamnatin jihar Kano ta yo hayar baki ‘yan daba daga kasashe makwabta, da wasu jihohi domin sabbaba rashin zaman lafiya a jihar Kano a daf da shiga zabe karo na biyu. Ba wai a iya nan kawai lamarin ya tsaya ba, wai sai da ta kai ma har fadar shugaban kasa wai sai da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yaje domin ganin Ganduje bai sake samun nasara ba.” [Duba Jaridar Daily Trust ta jiya lahadi, 19/05/2019]

Ya ku bayin Allah! Wannan duk soki-burutsu ne, sharri ne da kage da kazafi da magautan Sarki, makiyan sa, har kullun suke kokarin hada wa domin su samu hujjojin cin mutuncin sa da Masarautar Kanon!

Ya ku jama’ah! Ku sani, wadannan mutane sun sha alwashin sai sun zubar da mutuncin addinin mu da al’adunmu, kuma da karfin Allah da ikon sa ba zasu ci nasara ba.

Ina rokon Allah ya kare mutuncin addininmu da Sarakunan mu da Masarautun mu, amin.

Wassalamu Alaikum

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta. Kuma za’a iya samun sa a: gusaumurtada@gmail.com ko kuma a +2348038289761.

Share.

game da Author