An yi garkuwa da faston cocin ECWA da mabiya 15 a Kaduna

0

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da faston cocin ECWA da mabiya 15 a Dankande dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna.

Wannan abin tashin hankali ya auku ne ranar Lahadi da safe a lokacin da faston da mabiya ke ibada a cikin cocin.

Masu garkuwan sun tafi da faston mai suna Zakariya Ido, ‘ya’yan sa biyu da sauran mabiya 15.

Sakataren cocin ECWA na yankin Zaria, Nath Waziri ya tabbatar da haka inda ya bayyana cewa masu garkuwan sun far wa cocin ne yayin da faston da mabiya ke kammala ibada da suka kwana suna yi a cocin.

” Masu garkuwa sun far wa cocin dauke da bindigogi sannan suka kwace wayoyin mabiyan dake cikin cocin sannan suka tafi da faston da su duka 15.

‘YAN SANDA

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da labarin yin garkuwa da wani fasto da kuma mabiyan sa 14.

Da ya ke wa PREMIUM TIMES karin bayani ta wayar tarho, Kakakin Yada Labarai Yakubu Sabo, ya ce an kama mabiya addinin Kiristan ne lokacin da au ke kan hanyar komawa gida daga coci.

Ya ce an kama su ne a kauyen Jiti Odongawa, kusa da Unguwar Kuli da ke kan iyaka da Sabuwa da Birnin Gwari da ke iyaka da Jihar Katsina da Kaduna.

Jaridar The Nation ta buga labarin a ranar Lahadi, amma jami’an ‘yan sanda ba su ba jaridar tabbacin afkuwar garkuwa da mutanen ba. Kuma ba a tabbatar da sunayen su ba.

Sai dai kuma jiya Litinin an tabbatar wa PRWMIUM TIMES cewa baya ga fasto an yi garkuwa da maza hudu mata goma. Su 15 kenan.

Kakakin ‘Yan Sanda Sabo, ya ce ana ta neman su da neman wadanda suka yi garkuwa da su. Ya kara da cewa an sanar da rundunar fatattakar masu garkuwa da mutane, wadda ke karkaahin zakakurin dan sanda, Abba Kyari.

Share.

game da Author