An maka Cif Jojin Najeriya kotu, bisa zargin yin karyar yawan shekaru

0

Wani dan kasuwa dan shekaru 46, mai suna Tochi Micheal, ya maka Cif Jojin Najeriya, Babban Mai Shari’a Tanko Muhammad kotu, bisa zargin cewa ya kantara karyar yawan shekaru.

Micheal ya maka Cif Jojin ne kotu, a gaban Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya, Abuja.

Takardar karar mai lamba FCT/HC/BW/CV/79/2019, an shigar da ita a kotun ne tun a cikin watan Afrilu, inda Micheal ya yi ikirarin cewa Tanko Muhammed ya rage yawan shekarun sa na haihuwa.

Micheal ya ce Cif Joji ya yi karyar shekarun haihuwa, domin akwai inda ya rubuta cewa an haife shi a ranar 31 Ga Disamba, 1950, amma suka a cikin takardun sa na daukar shi aikinn shari’a, ya rubuta cewa an haife shi a ranar 31 Ga Disamba, 1953, maimakon 1950 kamar yadda ya ke a can baya, har ma a cikinntakardar shaidar jarabawar sa ta WAEC.

Daga nan sai mai karar ya nemi kotu ta sanar da shi shin wannan daidai ne ko laifi ne? Ya kuma nemi sanin cewa shin idan alkali ya kantara irin wannan karya, ya karya dokar kasa ko kuwa bai karya ta ba.

Micheal ya kuma nemi sani daga kotu shin Tanko bai karya alkawarin aikin alkalanci ba? Kuma shin bai karya ka’idar dauka aikin shari’a ba da ke shimfide a cikin Kundin Dokokin Najeriya?

Daga nan sai ya roki kotu da ta umarci Sufeto Janar na ’Yan Sanda ya gurfanar da Tanko a kotu domin a hukunta shi, daidai hukuncin da ya dace a yi wa wanda ya aikata laifi irin nasa.

Sai dain kuma lauyan Cif Joji mai suna Sam Ologunorisa, ya roki kotu ta yi watsi da karar, domin a jiya Talata da aka kira karar, babu mai kara kuma babu lauyan sa a kotun.

Sai dai kuma mai shari’a Danlami Senchi ya ce ba zai yi gaggawar korar karar ba tukunna. Ya bai wa mai kara da lauyan sa uzurin cewa za a sake zaman saurare a ranar Juma’a mai zuwa, don haka ya na sanar da su cewa su gabatar da kan su a kotu a ranar, domin fara sauraren kara.

Share.

game da Author