Ganin yadda farashin danyen man fetur ya zarce farashin da gwamnati ta yanka a cikin kasafin kudi na 2019, Kwamitin Kula da Tsare-tsaren Kudi na babban bankin CBN, ya gargadi gwamnatin cewa kada ta shantake ta fantsama bushasha da kudade.
Maimakon haka, ya kamata gwamnati a rika adana rarar ribar danyen mai a cikin asusun adana ribar mai, domin ajiya maganin wata rana.
A cikin wata takardar sanarwa da aka fitar jiya Talata a Abuja, bayan taron kwana biyu, an bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta rika tara kudaden rarar ribar danyen man fetur, domin cin moriyar su a lokacin da kasuwar farashin danyen mai ya yi kasa.
“An tsara kasafin 2019 a kan farashin gangar danyen mai daya dala 60. Sannan kuma an shimfida kasafin a kan ganga milyan 2.3 da gwamnati ta ce su hakowa na danyen mai a kullum.
“To yanzu tunda gangar danyen mai ta kai dala 70, dalili kenan MPC ta ce babu wata bukatar gwamnati ta yi giringidishin cewa tunda an samu karin farashin danyen mai, bari mu kara gejin kasafin kudi zuwa dala 69, 70, har ta rika rafkar kudade ta na kashewa afujajan.
“Idan aka samu kudin mai tsakanin dala 69 zuwa 72, to wajibinmu ne ta rika killace su ana adanawa domin ranar da farashin ka iya faduwa warwas, to akwai kudaden da za a cike gibi kenan.” Haka kwamitin ya fitar da sanarwar bayan taro.
Kwamitin ya kuma bada shawarar gaggauta karbo kudaden lamunin daga bankuna a inda aka fuskanci huldar hada-hada da masu taurin-bashi.