A yau ne za a fara zaman sauraren karar da Atiku Abubakar ya shigar a Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa.
Atiku ya yi takara tare da Shugaba Muhammadu Buhari na APC, inda ya yi rashin nasara.
Sai dai ya ki amincewa da rashin nasarar, inda shi da jam’iyyar sa PDP suka shigar da karar kalubalantar INEC, APC da kuma Buhari.
Akwai ma wasu jam’iyyu hudu da suka shigar da karar rashin amincewa da sakamakon zaben baya ga PDP.
Karar da Atiku ya shigar ta dauki sabon salo da kuma daukar hankali a lokacin da shi da PDP suka ce bas u amince da Shugabar Kotun Daukaka Kara, Zainab Bulkachuwa ta shugabanci rukunin Alkalan da za su yi shari’ar karar da ya shigar ba.
Lauyoyin Atiku sun ce Zainab ba za ta yi musu adalci ba, domin ta na da alaka ta kut-da-kut da jam’iyyar APC.
Mijin Zainab, wato Muhammed Bulkachuwa, ya na daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, kuma ya fito takarar sanatan Jihar Bauchi a karkashin APC, ya kuma yi nasara.
PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda abokin takarar zaben fidda-gwanin APC na sanata da Muhammed Bulkachuwa, wato Yusuf Maitama-Tuggar ya yi korafin cewa an tafka masa magudi, aka murde sakamakon nasarar sa, aka ba Muhammed Bukachuwa.
Korafi na biyu da Atiku a kara yi, shi ne dan Zainab Bukachuwa ma na cikin ta, shi ma rikakken dan jam’iyyar APC ne, domin har takarar zaben fidda-gwani na takarar gwamna sai da ya fito.
Lauyoyin Atiku sun gabatar da shaidar fastoci da kuma yadda dan Zainab ya rika tallata kan sa da yadda aka rika tallata shi a shafin sa na Facebook.
SANARWAR ‘YAN SANDA
Jami’an tsaro na ’yan sanda sun yi sanarwar cewa saboda tsammanin cinkoson jama’a da za su halarci kotun, ta na kira da masu motoci su kaurace wa Titin Goodluck Ebele Jonathan da kuma babban Titin Shehu Shagari.
Dukkan wadannan titina sun a kusa da Babbar Kotun Daukaka Kasa, inda alkalai biyar za su yi shari’ar hukucin zaben shugaban kasa da PDP da wasu jam’iyyu biyar suka maka APC, Buhari da kuma INEC kara.
Rundunar ’yan sanda ta ba jama’a hakuri bisa ga takurar da za su fuskanta domin kokarin kewayewa daga bin wadannan titina guda biyu.