A ranar Litini ne wani Dan-Sumogal da ake zargin shigowa da shinkafar da gwamnati ta hana shigowa da shi kasar nan ya bankade wani ma’aikacin hukumar kwastam mai suna Azeez Tunde-Wasiu da mota har lahira.
Kakakin hukumar Isa Dan-Baba ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata.
Dan-Baba yace Wasiu ya gamu da ajalinsa ne a wajen kokarin kama wannan mutumin da suke zargi da shigowa da shinkafa da karfe 11 na safiyar Litini.
“ Wasiu tare da wasu ma’aikatan hukumar a cikin mota mai kirar Peugeot 406 sun biyo wannan dan-Sumogal ne dake mota mai kira irinta Golf daga Sule Tankarkar zuwa cikin garin Gumel. Da suka kai titin Emir’s Palace sai Wasiu ya fice daga motar domin yi wa wannan mutumin barazanar harbe sa da bindiga idan bai tsaya ba.
“Ganin haka kuwa sai wannan mutumi ya ja motar sa da gudu ya bankade Wasiu.
Dan-Baba yace mutum ya kuma kade wasu ‘yan achaba biyu masu suna Usman Abdu mai shekaru 32 da Adda’u Dahiru mai shekaru 29 yayin da yake kokarin gudu.
‘Yan achaban na kwance a asibitin Gumel.
Dan –Baba yace hukumar na zargin cewa motar da wannan mutumi ya gudu da shi na dauke da shinkafan da gwamnati ta hana shigowa da shi kasar nan kuma hukumar na da labarin cewa mutumin ya shigo da shinkafar ne daga kasar Niger a hanyar sa ta zuwa Kano.