Akalla mutane 26 aka bada rahoton sun rasa ran su, a wani hari da Boko Haram suka kai kauyen Kudakaya, cikin Karamar Hukumar Madagali, a Jihar Adamawa.
Harin wanda aka kai jiya Litinin, ya yi sanadiyyar ji wa wasu da dama raunuka sakamakon farmakin na Boko Haram.
Mazauna karkarar sun tabbatar da cewa maharan Boko Haram sun yi wa garin dirar fari-dango a kan babura, kuma an tabbatar da cewa su na da yawan gaske.
Sun isa ne da misalin karfe 7 na yamma.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa, Othman Abubakar ya tabbatar da kai harin.
“An sanar da ni tabbatacin kai harin wanda Boko Haram suka kai a kauyen. Amma ya zuwa yanzu ban kai ga samun takamaimen yawan wadanda suka rasa rayukan su ba. Amma an tura jami’an tsaro kuma su na gudanar da abin da ya kamata a wajen.”
Wannan yanki dai ya sha fama da hare-haren Boko Haram sau da dama a watannin da suka gabata zuwa jiya Litinin da aka kai musu hari na baya-bayan nan.
Wani dan sintirin bijilanti, wanda ya ki bada sunan sa, ya ce ya kirga gawawwaki 26, sannan kuma wasu mutane masu yawa sun ji raunuka.
Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Madagali, Abawu Ularamu, ya kara tabbatar da abin da dan sintirin ya ce ya gani da idon sa.
Sannan kuma ya kara da cewa: “Sun kuma kone shaguna da yawa, sun kona gidaje, suka saci kayan abinci.”
Haka Ularamu ya shaida wa PREMIUM TIMES.
“Ko shakka babu, maharan daga cikin Dajin Sambisa suka fito, domin sun sha kawo mana hari a kai a kai, inda sukan sace mana kayan abinci.”
Discussion about this post