GARABASA: Sanatoci da ’Yan Majalisar Tarayya za su karbi alawus da garatutin naira biliyan 23.7

0

Sanatoci na Mambobin Majalisar Tarayya za su karbi jimlar kudaden sallama har naira biliyan 23.7 tare da sauran alawus-alawus.

Wadannan makudan kudade za a bayar da su ne a matsayin kudaden sallama ga wadanda suka kammala wa’adin su.

Haka kuma su na cikin alawus din da za a raba wa sabbin-yanka-raken wadanda za a rantsar cikin wata mai zuwa, da kudaden masu hidimta musu a ofis idan sun shiga.

Wadanda za su shigo su ne za su kasance Zangon Majalisa na 9. Zango na 8 ne karkashin Bukola Saraki da Yakubu Dogara za su kammala wa’adin su a ranar 28 Ga Mayu, 2019.

Wadannan adadi na cikin Kasafin 2019 wanda Majalisa ta mika a zaman kudirin doka.

Kudaden a jimlace sun kama naira bilyan 23, 678, 770,079.

An ware wa Majalisar Dattawa da Tarayya kasafin naira bilyan 139.5 a 2018.

Majalisar Dattawa aka raba wa bilyan 35, ita kuma ta Tarayya naira biliyan 57.

Hadiman da ke taimaka musu kuma sun lashe naira bilyan 10, shi kuma ofishin na su an ware masa naira bilyan 15 a matsayin kudaden gudanarwa.

Hukumar Kula Da Majalisar Tarayya kuma nan kashe mata naira biliyan 2.

An ware wa Cibiyar Horas da Ma’aikatan Majalisa har naira bilyan 4. 4.

Share.

game da Author