Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa zai ci gaba da caccakaer Shugaba Muhammadu Buhari har sai ya inganta tsarin salon tafiyar da gwamnatin sa.
Ya kara da cewa ya na da cancantar da zai soki lamirin ko ma wace gwamnati matsawar shugaban ta ya na kaucewa daga tafarkin da ya dace ya jagoranci al’umma da kuma kaucewa kan tsarin gudanar da ayyukan da suka wajaba ya gudanar.
Haka Obasanjo ya bayyana a lokacin da ya ke jawabi wurin taron laccar taya shi murnar cika shekaru 82 a duniya, wanda aka gudanar a Abeokuta.
Obasanjo ya bude wannan wuta ce jim kadan bayan da babban basarake Alake na Egbaland, Adedotun Gbadebo ya shawarci Obasanjo din da ya daina caccakar Buhari haka nan.
Tsohon shugaban kasar ya dade ya na sukar gwamnatin Buhari, wadda da farko ya goya wa baya. Daga baya kuma ya koma bayan Atiku Abubakar, dan takarar jam’iy\yar PDP a zaben shugaban kasa na 2019.
Alake ya roki Obasanjo ya yi wa Allah ya daina sukar gwamnatin Buhari.
“Kun san lokacin da ina soja, ina karkashin Janar Buhari, to a yanzu kuma a duk lokacin da Obasanjo ya ragargaji Buhari, na kan ce masa, ‘haba ogan mu, ka kyale shugaban kasa haka nan mana.
Yanzu ka na da shekaru 82, haba Baba, ka yi hakuri ka maida wukar ka cikin takobi mana. A matsayin ka yanzu ba na fada da mutane ba ne, sai dai ka rika bada shawara.” Inji basarake Alake.
Obasanjo ya maida masa da martanin cewa shi fa ba shi da wata nifaka da Buhari, amma kowa ya sani a tafarkin dimokradiyya ai kowa na da ‘yancin yin suka ga shugaban da aka ga baya yin abin da ya kamata, ko abin a zo a gani.
Obasanjo ya ce a tuna fa har yau har kwanan gobe shi ne shugaban da ya fi dadewa ya na mulkin Najeriya. Don haka babu wani dare da jemage bai gani ba.
“Don haka ni ba da ka na ke magana ba.
idan na fadi abu to na san abin da na ke fadi. Idan na ce wannan gwamnati ba ta yin wani abin kirki, ko kuma ta kauce, to wanda ya ke ganin magana ta ba kan hanya ta ke ba, sai ya fito ya bayar da hujjojin cewa gwamnatin a kan turba ta ke mana.” Inji Obasanjo.
“Ran Sarki ya da dade ni ba ni da wata nifaka ko haushi ga ogan ka Buhari, kurakuran da ya ke tafkawa ne na ke yin suka a kan su.” Inji Obasanjo
Discussion about this post