Babbar Kotun Tarayya a garin Jalingo ta tsige dan takarar gwamnan APC na jihar Taraba, Sani Danladi.
Rahoton da wasu jaridu ciki har da Daily Post suka buga ya ce an soke takarar Danladi ne bisa dalilin kantara karyar adadin shekarun sa.
Nan da nan dai jam’iyyar APC an yanke hukuncin ne domin a tsinka wa jam’iyyar APC jaka a ranar biki.
Aaroon Artimas sakataren yada labarai na APC a jihar Taraba ta sanar da haka.
Ta ce wasu mutane ne da ba a san ko su wa ba ne suka shigar da karar Sani Danladi cewa ya yi wa INEC karyar adadin shekarun sa.
APC ta ce an taba kai Danladi kara a cikin 2007 dangane da karyar shekaru, kuma Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da shari’a.
Kan haka sai APC ta ce, tunda Kotun Daukaka kara ta taba watsi da karar, ai babu wata kotu kuma da za ta sake tayar da maganar.
Daga nan sai APC ta ce kowa ya yi biris da wannan hukunci, a ci gaba da kamfen domin sun shigar da kara kuma jam’iyyar na da yakinin cewa za a jingine wannan hukunci da Babbar Kotun Tarayya ta yi.
Discussion about this post