ATIKU YAYI NASARAR FARKO: Kotu ta umarci hukumar zabe ta mika wa Atiku kayan Zabe domin yin bincike

0

Kotun daukaka kara ta umarci hukmar zabe ta mika wa Atiku Abubakar da jam’iyyar sa ta PDP takardu da na’urorin da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa da aka yi domin bin diddigin yadda aka yi zabe a kasar nan.

Alkalin kotun da ya yanke wannan hukunci Abdul Aboki ya bayyana cewa dokar Zabe ta yarda wa duk wanda ya ke da korafi bisa ga sakamakon zabe ko kuma yadda aka gudanar da zabe da a bashi damar bincikar takardun zaben da aka yi amfani da su da kuma na’urorin da aka yi amfani da.

Sai dai kuna duka alkalai uku da suka yi zaman yanke wannan shari’a sun ki amincewa da neman a yi binciken keke-da-keke ta yadda za a bi kowacce kuri’a da aka kada da ita kanta na’urar tantance masu kada kuri’a.

Bayan haka kotun daukaka karar da ita ce kotun da za ta saurari korafe-korafen zaben shugaban kasa ta ce ba za ta amince da a mika wasu takardun da aka shigar da sakamakon zabe ba domin ayi bincike sannan kuma kotun bata amince a mika na’urar da aka yi amfani dasu wajen shigar da sakamakon zabe ba ga Atiku domin yin binciken keke-da-keke.

Ta ce wannan dama ba zai tabbata wa PDP da Atiku ba kamar yadda suka nema domin doka bata amince da yakai ga haka ba.

Idan ba a manta ba tun bayan da aka bayyana sakamakon zaben shugaban kasa ne dan takarar PDP Atiku Abubakar ya ce bai yarda da sakamakon ba inda tuni ya garzaya kotu.

Atiku ya sha kayi ne a zaben a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC.

Atiku ya ce an tafka magudi da murdiya a zaben da ya sa bai yi nasara ba.

Share.

game da Author