ZABEN GWAMNONI: Ko Ka Ci Ko Ka Ci Kukan Zuci, Bi mu Kai Tsaye a nan

0

PREMIUM TIMES ta yi shiri tsaf domin kawo wa dimbin masu karatun ta labarai, rahotanni da bayanan sakamakon zaben gwamnoni kai-tsaye.

Wannan zabe na gwamnoni da majalisar dokoki zai zama zaben zaben kai-da-halin-ka. Domin dai alamomi sun nuna cewa ba duk wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a zaba ne za a rufe ido a zabe shi ido rufe ba.

Shi kan sa Buhari ya furta cewa kowa ya zabe wanda ran sa ya kwanta masa. Wannan kuwa zai ba jama’a da dama damar huce-haushin su a kan wasu gwamnoni, musamman wadanda suka rika gajiyar da su kafin biyan su albashi da wadanda suka ki yarda a yi karin albashin.

Wani abin dubawa dangane da wannan zabe, shi ne ba a kowace jiha cwe gaba daya 36 za a yi zaben ba. Ba a yi zaben gwamna a jihohin Kogi, Osun, Ekiti da Ondo ba. Saboda gwamnonin da ke kai bas u cika shekara hudu a kan mulki ba. amma kuma za a yi zabukan majalisar dokoki a jihohin.

Jihohin da jama’a za su fi bada hankali a zaben gwamna sun hada da: Kano, Kaduna, Lagos, Akwa Ibom, Rivers da Taraba.
Akwai kuma Jigawa, Enugu da Imo da Gombe da Oyo da kuma Sokoto.

SOKOTO:

Wakilin mu ya ci karo da dandazon jagororin Jam’iyyar APC da magoya bayan su suna siyan Kuri’u a boye. Wani da ya tattauna da wakilin mu ya ce duk wadanda suke da katin zabe na dindindin ne ake biya wadannan kudade domin siyan kuri’un su.

Ya kara da cewa ana biyan daga naira 3000 zuwa har 700.

An samu wadannan masu rabon kudi ne cikin daren Juma’a zuwa wayewar asabar din yau.

KADUNA:

Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kaduna Abdullahi Kaugama ya bayyana cewa za a yi amfani da na’urar tantance katin masu zabe ‘Card Reader’ har 3,008 a zabe a Kaduna.

Kaugama ya fadi haka ne da yake ganawa da manema labarai a ofishin hukumar dake unguwar Rimi a Kaduna ranar Juma’a.

Ya kuma jadadda cewa hukumar zabe za ta soke zaben da aka yi a rumfar da na’urar ‘Card Reader’ bai yi aiki ba.

” A dalilin haka muke kira ga mutane da su kwantar da hankulan su bi ma’aikatan mu sannu a hankali tare da tabbatar cewa na’urar ‘Card Reader’ na aiki kafin su jefa kuri’un su.

DAURA:

Da misalin karfe takwas na safiyar yau Asabar ne shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da uwargidan sa Aisha suka nufi rumfar zabe 003 dake Gidan Niyam a Daura jihar Katsina domin jefa kuri’un su.

Da karfe 8:08 bayan an kammala tantance su shugaba Buhari tare da Aisha suka kada kuri’un su.

HOTUNA:

KADUNA:

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba zai damu ba ko da ya fadi zaben gwamna da ake kan gudanarwa yau Asabar.

“ Ni ba ni wani zaman dardar din jiran sakamakon zabe. Mafi munin abu dai ai a ce na fadi zabe. To idan na fadi ba ni da kaico, tunda dai Shugaba Muhammadu Buhari ya rigaya ya ci zaben shugaban kasa, to bukata ta biya.”

“Ma’aikata na da makusanta da hadimai na ne ke kwana cikin fargaba. Amma ni ban damu ba.”

Haka ya shaida wa manema labarai bayan ya jefa kuri’ar sa da karfe 8:30 na safe, a rumfar zaben sa da ke Unguwar Sarki, Kaduna.

BAUCHI:

Rikici ya kusa barkewa a jihar Bauchi inda mutane suka gano cewa kayan zaben da ya kamata a raba wa rumfunar zabe uku an hada su a rumfa daya.

Hakan na nufin cewa an soke biyu daga cikin rumfunar zabe uku dake Senator Abubakar Maikafi Crescent sannan aka mayar da rumfar zaben a makarantar nazare da firamare dake Makama.

BENUWAI:

An kama Emmanuel Jime, dan takarar gwamnan jihar Benuwai na APC dauke da jakunkunan kudi a ranar zabe.

EFCC ne suka kama Jime a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa sayen kuri’u.

An kama shi ne a daidai mazabar North Bank da ke Makurdi, babban birnin jihar.

Rahotanni kuma sun tabbatar da cewa ‘yan takifen da ke goyon bayan dan takarar gwamnan sun kai wa motocin EFCC hari a bisa yunkurin su na hana su yin aikin su.

Hukumar EFCC ta yi sanarwar kama dan siyasa ya na kokarin sayen kuri’u, amma ba su ambaci sunan sa a shafin su na twitter ba.

EBONYI: ’Yan takife sun banka wa Ofishin INEC wuta a Jihar Ebonyi

Wasu ‘yan takife sun banka wuta a ciniyar rajisrar INEC da ke Karamar Hukumar Ezza ta Arewa a jihar Ebonyi.

Lamarin ya faru jiya dare ranar Juma’a. ofishin ya kasance cibiya ce da INEC ke amfani da ita wajen tabbatar da cewa ta rarraba kayan zabe a sauran yankunan da ke kewan karamar hukumar.

Jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas a Najeriya, ta kasance jihar da aka sha fama da tashe-tashen hankula gabanin zaben shugaban kasa. An ruwaito mutuwar mutane biyu a lokacin.

Share.

game da Author