Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kaduna Abdullahi Kaugama ya bayyana cewa za a yi amfani da na’urar tantance katin masu zabe ‘Card Reader’ har 3,008 a zabe a Kaduna.
Kaugama ya fadi haka ne da yake ganawa da manema labarai a ofishin hukumar dake unguwar Rimi a Kaduna ranar Juma’a.
Ya kuma jadadda cewa hukumar zabe za ta soke zaben da aka yi a rumfar da na’urar ‘Card Reader’ bai yi aiki ba.
” A dalilin haka muke kira ga mutane da su kwantar da hankulan su bi ma’aikatan mu sannu a hankali tare da tabbatar cewa na’urar ‘Card Reader’ na aiki kafin su jefa kuri’un su.
‘‘A yanzu dai mun kammala kara horas da ma’aikatan wucin gadin da za su aiki sannan mun dauki matakan da za su taimaka mana wajen ganin zabe ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Kaugama yace bashi da masaniya game da ‘yan takarar da suka sauka daga takara domin sharewa wani dan takara fage.
” ‘Yan takara 38 ne ke takarar kujerar gwaman kuma ‘yan takara 396 ne ke takarar kujerun majalisar dokoki na jihar.
Ya ce hukumar zabe ta kammala raba kayan zabe a duk kananan hukumomi 23 dake jihar.
‘‘Ma’aikatan wucin gadi 34,000 ne za su yi aikin zabe inda daga ciki 10,000 masu yi wa kasa hidima ne. Sannan mu fara gudanar da bincike domin kamo wadanda suka musanya ma’aikatan wucin gadin da muka horas da wadanda basu da horo akan aikin.