BAUCHI: Jami’an tsaron da basu aiki ranar zabe su nisanta kansu daga rumfunar zabe – Rundunar ‘yan sanda

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi Ali Janga ya yi kira ga duk jami’an tsaron da doka ba ta amince masa da yin aiki ranar zabe ba da ya nisanta kansa daga runfunar zabe ranar Asabar.

Jangana ya fadi haka ne wa manema labarai a hedikwatr rundunar ranar Juma’a a garin Bauchi inda ya kara da cewa jami’an tsaron da doka ta amince musu fito a lokacin zabe ne kawai za su tsaya a rumfunar zabe.

” A dalilin haka muke kira ga kungiyoyin ‘yan banga,mafarauta da sauran su da su nisanta kan su daga rumfunanr zabe ranar Asabar.

Ya kuma ce rundunar ‘yan sanda ba za ta amince wa duk wani dan siyasa ya zo rumfar zabe da masu gadinsa ba sannan ya kuma kara yin kira ga ‘yan siyasa da su guji yawo daga rumfar zabe zuwa wata rumfar a ranar zabe domin guje wa tada rikici.

Jangana yace rundunar ba za ta yi kasa kasa ba wajen ganin ta kama kuma ta hukunta duk ‘yan jagaliyar da ke kokarin tada rikici a jihar ranar zabe.

Bayan haka rundunar ‘yan sandan ta kuma sanar da hana zirga zirgan mutane da ababen hawa daga karfe shida na safe zuwa shida na yamman Asabar.

Ya ce jami’an tsaro za su kyale wadanda zirga zirga a wannan rana ya zama wa dole ne kawai idan suna rike da katin shaidar su daga hukumar zabe ko kuma wuraren aikin su.

Jangana ya yi kira ga shugabanin addinai,sarakunan gargajiya da iyaye da su tabbata sun ja kunnen yara da matasa kan guje wa tada rikici a ranar zabe.

Share.

game da Author