Ko hanyar zuwa Kano ban bi ba, ballantana ace an ganni a cikin ta – Inji Tinubu

0

Ofishin Jagoran Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ya je Kano domin ya taya Gwamna Abdullahi Ganduje shirya yadda zai ci zaben da za a maimaita a wasu wurare a jihar, ranar Asabar mai zuwa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labaran sa, Tunde Rahman ya sa wa hannu, kuma ya aiko ofishin PREMIUM TIMES a jiya Talata da dare, Tinubu ya ce bai je Kano ba, kuma ko hanyar zuwa Kano bai bi ba, ballantana a ce har an gan shi a cikin Kano.

Ya kara da cewa masu watsa hotuna na karya cewa Tinubu ya je Kano, sun san ba gaskiya ba ne.

“ Bari na tantance muku tsaki da kuma tsakuwa, Asiwaju bai je Kano a ranar zabe ko bayan zaben Kano ba. Hoton da ake yadawa a soshiyal midiya an dauke shi ne a lokacin da Gwamna Ganduje ya kai masa ziyara a Legas, tun cikin 2018.

“Ina girmama mutanen Kano, kuma ina jinjina wa yanayin takun siyisar su. A koda yaushe zabin su shi ne su zabi masu ra’ayin kawo sauyi a siyasa, shi ya sa suka zama jigo da turken zaben Shugaba Muhammadu Buhari a karkashin jam’iyyar APC.”

Tinubu ya ci gaba da cewa tilas idan ana maganar siyasa a kasar nan, sai an jinjina wa mutanen Kano.

“Amma kuma bai kamata don wasu ‘yan PDP na neman wata biyan bukata ba, sai sun nemi su goga wa Asiwaju Tinubu kashin-kaji ba. To ku sani Tinubu bai je Kano kafin zabe da kuma bayan zabe. Don haka tunda bai taba tandu ba, kada wanda ya goga masa maiko a jiki.”

Takardar ta kuma nuna rashin kyautawar da wasu ’yan PDP suka yi wa Tinubu, inda suka kau da kai daga yadda Atiku da Bukola Saraki suka yi katsalandan a zaben jihar Legas.

“Masu kantara wa Tinubu karyar cewa ya je Kano, idon su ya rufe, ba su kalli abin da Atiku da Saraki suka yi na katsalandan a zaben Legas ba. Sai dai kuma katsalandan din na su bai amfane su ba, domin kowanen su ya koma gida buhun-kunya.” Inji takardar.

A karshe yace bai shiga cikin batun zaben Kano da za a sake ba, kuma ba zai shiga ba. Ya ce Kanawa abin da ran su ke so, shi su ke zabe, ba a sa su kuma ba a iya hana su.

Share.

game da Author