Kakakin Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar, Buba Galadima, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta yi amfani da karfin soja ta murde zaben shugaban kasa na 2019.
Galadima ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke hira da Gidan Talbijin na Channels, inda ya ce abin da kawai ya faru a jihar Ribas ya isa duk mai hankali ya amince cewa an yi amfani da sojoji wajen firgita jama’a.
“Wannan ba wai zargi ne ake yi musu ba, sojoji sun tafka ta’asar da idan aka maka su Kotun Hukunta Masu Manyan Laifuka ta Duniya, to ba su da mafita.” Iinji Galadima.
“Da ido na na kalla a cikin talbijin yadda sojoji suka rika bi gida-gida su na karkashe mutane.”
Da farko APC ta ce jam’iyyar PDP ta hada kai da INEC aka bayyana kirkirarren sakamakon zabe a jihar Ribas.
Galadima ya ce akwai hujjoji da dama da suka nuna cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin watan Fabrairu, kuma hujjojin sun nuna cewa APC magudi ta tabka.
“Su da suka ce sun yi nasara, to me kuma na neman zuwa kotu su binciki kayan zabe? Wannan zai nuna maka cewa dama can magudi da murdiya suka yi.”
“Na san abin da na ke fada, kuma iyakar gaskiyar abin da ya faru kenan. Ko a gaban kotu zan iya tabbatar da hujjojin cewa an yi magudi da murdiya.”
Kai ka taba jin inda wanda ya yi nasara ta gaskiya da gaskiya ya garzaya kotu neman binciken kayan zabe?
PDP da Atiku sun ce na’urar killace sakamakon zabe ta INEC ta nuna cewa Atiku ya na gaba da Buhari da ratar kuri’u milyan 1.6.
Galadima ya kuma zargi APC da biyan wasu manyan Najeriya makudan kudade domin su roki Atiku kada ya kai kara kotu.
“Duk da Kotun Koli ta zartas da cewa Buhari ya fadi a zaben 2003, 2007 da na 2011, kai ka taba jin ya taya wadanda suka yi nasara murna?” Inji Buba Galadima.