Babban Lauya mai jagorantar lauyoyin Atiku Abubakar a karar da ya shigar kan zaben 2019, ya ce sun tanadi kwarara kuma gamsassun hujjojin da za su iya wadatar da Kotun Daukaka Kara ta tsige Shugaba Muhammadu Buhari daga kujerar mulki, bisa haramcin zaben 2019.
Haka babban lauya Livy Uzoukwu ya shaida a ranar Litinin, a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a Abuja, jim kadan bayan ya ja zugar tawagar lauyoyin Atiku suka kai bayanan korafe-korafen su a kan zaben 2019, a gaban Kotun Daukaka Kara.
Sun gaggauta shigar da karar ce saboda ganin cewa kwanaki 21 na wa’adin shigar da karar zaben da abokin takara bai gamsu ba sun kusan cika, kamar yadda Sashe na 134 na Dokar Zabe ta 2010 ta gindaya.
An shigar da karar ce wadda Atiku da kan sa ya sa hannu a matsayin mai kara, shi da jam’iyyar PDP.
Wadanda ake kara sun hada da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), APC da kuma Buhari.
Uzoukwu ya ce ya na da yakinin cewa Atiku da PDP za su yi nasara a kotu, domin dama tun farko su ne suka yi nasara a zaben, ba APC ba.
Za a fara kuma a karkare tare da yanke hukuncin wannan shari’a a cikin kwanaki 180, kamar yadda Dokar Zabe ta tanadar.