Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce za ta biya kudin ladar aikin zabe naira 30,500 ga dukkan masu bautar kasa (NYSC) da suka shiga aikin zabe.
Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Laraba a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi dangane da sabbin shirye-shiryen da aka samu wajen gudanar da zabe a ranar Asabar mai zuwa.
Yakubu ya ce za a biya kowane dan NYSC alawus na ladar aikin sa, naira 30,500.
Wannan bayani ya zo ne kwana daya bayan da wasu masu bautar kasa da za su yi akin zabe suka rika watsa labarin cewa an fara biyan kudin alawus na INEC, amma akwai bambancin yadda aka biya wasu ya sha bamban da abin da aka biya wasu.
An ruwaito cewa a ranar Juma’ar da ta gabata, da dama daga cikin su sun kai kan su wuraren da za su yi aiki ne bayan da INEC ta yi jinkirin biyan su kudaden alawus na tirenin har naira 4,500 da aka yi musu alkawari.
Wannan ya sa masu bautar kasa suka rika yada barazanar cewa idan ba a biya su kudaden ba, to ba a su yi aikin zaben ba.
Sun rika watsa wannan bayani a wani zauren su na WhatsApp.
Wannan ya sa nan da nan aka fara biyan su, kuma suka yi sanarwar cewa an fara biyan su alawus na tirenin din, watau naira 4,500.00
Sai dai kuma ya zuwa jiya Laraba, wasu jihohin ne suka fara samun ‘alert’, wasu kuma ba su kai ga samu ba.
INEC dai gaba daya za ta biya ladar zuwa horaswar sanin makamar aiki ta naira 4,500. Kenan a zaben shugaban kasa da majalisar dattawa da ta tarayya, za su karbi naira 17,500.
Sai kuma sai zaben gwamna da na majalisar jiha, za a biya su naira 13,000. Gaba daya kudin sun kama naira 30,500 kenan.
Yakubu ya ce an tanadar wa kowane dan bautar kasar da zai yi aikin INEC kayan katifun kwanciya da mayafi da kayan wanka da bandakuna da kuma wutar lantarki da jami’an tsaro a cibiyoyin zaben da aka tura kowanen su.
Ya ce duk an tanadar musu da wadanan idan su ka isa wuraren a jajibirin ranar zabe, duk za a raba musu kayayyakin.