EFCC ta yi ram da Daraktan SSS da ke harkalla tare da Lawal Daura

0

Jami’an EFCC suna can suna sheka ruwan tambayoyi da bincike ga Mataimakin Daraktan Kudi na Hukumar SSS. Wata majiya ce daga EFCC ta tabbatar wa PREMIUM TIMES da wannan labarin.

Majiyar ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa kafin a fito da Kunle Kadri daga gidan sa, sai da aka cumuimuye shi aka garkama masa ankwa a hannayen sa. Kuma yanzu haka ya na can a na tsare da shi a hedikwatar EFCC, a Abuja.

Har yanzu dai jami’an EFCC ba su ce komai dangane da kama jami’in kula da hada-hadar kudade ta SSS ba.

Amma dai kwakkwarar majiya ta tabbatar da cewa an gano wata harkalla, asarkala, rub-da-ciki da karma-karma a fannin tasarifin kudade, wadanda aka alakanta cewa da Sanin korarren Daraktan SSS, Lawal Daura aka yi kumbiya-kumbiyar kudaden.

An ce Lawal Daura a yanzu haka ya bude fankamemen ofis a Maitama, cikin Abuja, inda ya ke fantamawa, kuma ya na gudanar da ayyukan tuntuba ga wannan gwamnati, wanda ke ta kai gwauro ta na kai mari wajen ganin ba ta fadi zaben shugaban kasa da za a gudanar jibi Asabar mai zuwa ba.

Kadri na daya daga cikin na-hannun-damar Lawal Daura kuma ya amince masa sosai. Ana kuma zargin har yanzu ya na da wata alaka ta boye da suke gudanarwa a asirce shi da Daura.

Majiya ta ce dangantakar ta su ta kut-da-kut ce, irin ta ‘abin da ya ci Doma, bay a barin Awai.’

Masu binciken kwakwaf a EFCC sun tabbatar cewa idan su ka taka ruwan cikin Kadri, to zai amayar da duk abin da ya sani dangane da badakalar da ta dabaibaye wasu kudade har naira bilyan 10.2 da SSS ta fara karba a matsayin kudaden biyan su ladar aikin zabe.

An gabatar da kasafin kudain wanda SSS ta ce za a kashe a Hukumar, tun a lokacin Lawal Daura na kan mulki. Amma an fitar da kudin a kwanan baya, lokacin da sabon Daraktan SSS, Yusuf Bichi ya hau mulki.

“Yan a bada hadin kai dangane da binciken da ake yi masa. Kasancewa ya yi aiki da Daraktocin SSS har uku da suka gabata, to ai ka ga babu wanda ya san lunguna da sakon da ake kurdawa da kudade kamar sa.” Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.

Har yanzun dai ko EFCC din ko kuma SSS, babu wanda ya fitar da wata sanarwa. Sai dai jiya Laraba SSS din sun fitar da gargadi cewa kada wanda ya kara yin wata huldar EFCC tare da Lawal Daura.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wannan gargadin a jiya Laraba.

PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin SSS, Afunaya, amma ya ce bai san da labarin kamun da aka yi wa Kadri ba. Ya ce idan akwai wani karin bayani zai yi daga baya.

Shi kuma kakakin EFCC, da aka kira wayar sa bai dauka ba, domin a ji ta bakin sa. Sakon kar-ta-kwan da aka yi masa, bai maida amsa ba.

Share.

game da Author