Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kama wata mota dankare da kayan zabe za a kaisu Sokoto daga Abuja.
Kwamishinan ‘yan sanda Celestine Okoye ya sanar da haka wa manema labarai a ofishin hukumar zabe dake garin Gusau.
Okoye ya ce bincike ya nuna cewa wasu ne da basu da izinin daukan kayan zabe suka loda wannan mota da kayan domin kai su jihar Sokoto.
” Ma’aikatan mu sun tare direban moton a wani shingen duba motoci daga nan sai yayi kokarin arcewa inda garin haka ya afka wa wasu masu tuka keke NAPEP guda biyu.
” Da motar ta tsaya sai ya yi kokarin kwashe wadannan kaya zuwa wata mota kafin mu su iso wurin.
Okoye yace rundunar ta kama motar da direban sannan ta na gudanar da bincike a kai.
” Ina kuma so na kara tabbatar wa mutane cewa jami’an tsaro ba za su yi kasa kasa ba wajen ganin sun kama duk wadanda bai kamata ya mallaki wani abu na zabe ba sannan sun dauki matakan da zai taimaka wajen ganin sun kare duk kayan zaben da za a yi amfani da su a lokacin zabe.
A karshe ita ma jami’ar hukumar zabe na jihar Asma’u Sani Maikudi ta tabbatar da haka.
A cikin makon nan ne hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta bayyana cewa ta dawo da kayan zaben da ta fara kaiwa wasu jihohi a kasar nan.
Hukumar ta yi haka ne domin tabbatar da inganci da sahihancin zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa, wanda za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.
PREMIUM TIMES ta bada labarin kalubalen da shugaban na INEC ya ce an fuskanta, wadanda tilas su ka sa aka dage zaben zuwa ranakun 23 Ga Fabrauru da kuma 2 Ga Maris.
Kungiyoyin rajin kare dimokradiyya irin su CDD, sun nuna tsananin damuwa ganin cewa yawancin kayan zaben duk an rigaya an tura su jihohi da kananan hukumomi kafin a soke zaben.
A kan haka ne INEC ta fara dawo da kayan zaben da aka rigaya a ka raba. Cikin jihohin da aka maida na su din akwai Lagos, Anambra, Enugu, Gombe da Filato.