Minista Shittu ya ce Oshiomhole ba shi da kimar da zai soki shugaban INEC

0

Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu, ya bayyana cewa Shugaban Jam’iyyar APC tantirin gogarman dan harkallar zabe ne, don haka ba shi da kimar da har zai iya fitowa ya ce Shugaban INEC ya sauka daga kujerar sa.

Minista Shitu a bayyana haka a gidan sa da ke Ibadan, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a jiya Litinin.

Idan ba a manta ba, Shittu ya nemi takarar gwamnan jihar Oyo, amma aka yi wancakali da shi tun a zaben fidda gwanin da ba a ma bari ya shiga cikin masu takara ba.

APC a karkashin Adams Oshiomhole ta ki tsaida shi a bisa dalilin rahoton da PREMIUM TIMES ta buga a baya cewa Shittu bai je aikin bautar kasa (NYSC) ba.

Ya ce cire Yakubu shugaban INEC saboda dage zabe, sai jawo wa hukumar zabe babbar matsala.

A kan haka sai Shittu ya ce ai idan ma aka cire shugaban INEC, to sai an sake dage zabe, domin sabon shugaban ya samu damar zaman da zai yi domin tsara sabon zabe.

“A lokacin da Oshiomhole ya shirya zaben fidda-gwani na ‘yan takarar APC, ai shi ne ya shirya zaben da ba a taba samun magudi mai muni a tarihin kasar nan, kamar lokacin da shi Oshiomhole din ya shirya na sa zaben ba.”

Zaben da Oshiomhole ya shirya ya samu kakkausar suka, ciki kuwa har da uwargidan shugaba Buhari, Aisha.

An yi zargin harkalla, cuwa-cuwa da cire mai gaskiya a maye gurbin sa da wanda ba shi ya yi nasara ba.

Rigingimun da aka haifar ne ya sa INEC da kotu suka hana APC shiga zabe a jihohin Rivers da Zamfara.

Shittu ya ce wannan ne karon farko da Yakubu zai gudanar da zabe na kasa baki daya. Don haka a ba shi uzuri ya yi zabe sahihi kuma ingantacce.

Share.

game da Author