SATAR AKWATIN ZABE: Sojoji sun ce za su bi umarnin Buhari su bindige mutum

0

Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta bi Umarnin Shugaba Muhammadu Buhari, matsawar ya bada odar cewa duk wanda ya fizgi akwatin zabe, to a bindige shi kawai.

Sun yi wannan karin haske ne biyo bayan kakkausan furucin da Buhari ya yi a jiya Litin cewa duk wanda ya saki akwatin zabe, to ya yi a ta bakin ran sa.

Wannan furuci ya janyo ce-ce-ku-ce da suka da caccaka, duk da dai magoya bayan shugaban na ta kokarin kare dalilan sa na yin furucin.

Dokar zabe dai ta tanadi daurin watanni 24 ga wanda aka kama ya arce da akwatin da aka jefa wa kuri’a.

Shi kuma Buhari ya ce a harbe wanda ya saci akwati ya tsere kawai.

Ya yi wannan kakkausan kalami ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC jiya Litinin a Abuja.

A na su bangaren, sojojin Najeriya sun kara wa wannan tankiya zafi, yayin da Kakakin su Sagir Musa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa idan dai shugaban kasa wanda kuma shi ne Babban Kwamandan Askarawan Najeriya gaba daya, ya bayar da oda ga sojoji, to babu tantama, ba tababa, kuma babu wani bata lokaci, aiwatarwa kawai za su yi.

Haka Musa ya shaida wa PREMIUM TIMES a lokacin da aka tambaye shi ko za su yi tunanin harbin wanda ya saci akwati ko a’a.

Hukumar Tsaro ta soja ta ce za ta zuwa jami’an ta, amma a wasu ayyukan da suka shafi lamurran zabe, ba har a kusa rumfunan zabe ba.

PREMIUM TIMES ta tuntubi rundunar ‘yan sanda domin jin ko su ma za su harbe barawon akwatin zabe ko a’a. Sai dai har yanzu ba su ce komai ba.

Buhari ya sake tsayawa takara ne inda zai goge raini da babban dan adawa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Sai dai kuma masu sukar lamarin Buhari sun ce furucin na sa babban hatsari ne sosai, domin ‘yan ta-kife za su iya amfani da kalaman sa su rika karkashe jama’a a lokacin zabe.

Share.

game da Author