Hukumar Tsaro ta SSS ta yi kakkausan gargadi ga ‘yan Najeriya da su daina kuma su guji yin duk wata mu’amala ta aikin da ya shafi harkar tsaro da tsohon shugaban hukumar, Lawal Daura, wanda aka kora a watannin baya.
SSS sun ce sun gaji da korafe-korafen da tozarta su da ake yawan yi cewa wai har yanzu Lawal Daura na fada-a-ji a hukumar SSS.
Mataimakain Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya cire Daura a ranar 7 Ga Agusta, 2018, bayan rikicin abin kunyar da SSS suka yi inda suka kewaye Majalisar Dattawa, a wani yunkurin canja shugabannin majalisar ta bayan gida, da bai yi nasara ba.
Rudanin ya faru ne a lokacin da Shugaba Buhari ya tafi Landan domin yin hutun ganin likita.
Kwanan bayan an rika yada ji-ta-ji-tar cewa har yanzu Lawal Daura na zaune a gidan gwamnati a cikin rukunin gidajen SSS, ya na shiga cikin harkokin hukumar tsundum.
Sai dai kuma wannan sanarwa da SSS suka fitar a yau Talata da safe, duk ta karyata wadancan zarge-zargen, kuma ta gargadi jama’a da su daina mu’amala da shi da sunan aikin SSS.
Kakakin SSS, Peter Afunaya ne ya sa wa sanarwar hannu.
Hukumar ta ce ba za ta lamunci a rika yi mata sojan-gona ko shisshigi a cikin aikin ta ba.
Discussion about this post