SIYASA ROMON JABA: Jam’iyyar Okorocha ta ce Atiku za ta zaba ba Buhari ba

0

Karin maganar nan da Hausawa ke cewa siyasa romon jaba, ga kitse ga kuma wari, ta kara tabbata a Jihar Imo, yayin da jam’iyyar AA ta bayyana cewa Atiku Abubakar za ta zaba a zaben shugaban kasa ba Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Kenneth Udeze ne ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin.

“Mu Atiku za mu yi, kuma mu na farin cikin yin aiki tare da duk wadanda suka yi amanna da tsarin federaliyya na gaskiya domin tabbatar da nagartacciyar gwamnati, musamman a wannan zabe mai zuwa.

Ya ce sun yanke shawarar zaben Atiku, ba za su zabi Buhari ba.

Yakuma kara jaddada cewa wannan ne matsayar gamayyar sauran jam’iyyu, wato CUPP.

BILUMBITUWAR OKOROCHA DAGA WANNAN JAM’IYYA ZUWA WACCAN

Idan ba a manta ba, gwamna Okorocha ne ya kafa jam’iyyar AA cikin 2005, kuma ya yi niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar cikin 2007.

Da shi aka kafa jam’iyyar PDP, wadda a karkashin ta ne ya tsaya takarar gwamna a 1999, amma Achike Udenwa ya kayar da shi a zaben fidda gwani, kuma ya yi nasarar zama gwamnan Imo.

Okorocha ya fice daga PDP, ya shiga APP, ya fito takarar shugaban kasa, a cikin 2003.

Bayan wasu ‘yan shekaru, ya kafa AA, har ya nemi fitowa takarar shugaban kasa, amma daga baya ya canja tunani, ya koma PDP.

Bayan komawar sa PDP, ya fito takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani, amma marigayi shugaba Umaru Yar’Adua ya kayar da shi, shi kuma ya zo na biyu.

Cikin 2007 ya nemi zama shugaban jam’iyyar PDP.

Sai dai kuma ya koma APGA, ya tsaya takarar gwamna kuma ya yi nasara a cikin 2011.

Kafin zaben 2015, Okorocha ya shiga cikin gamayyar jam’iyyun da suka kafa APC, inda ya sake tsayawa takarar gwamna karkashin APC, kuma ya yi nasara.

A cikin APC din ma sai da ya nemi zama shugaban kasa, amma a zaben fidda gwani a Lagos, ya zo na hudu.

Sai dai kuma duk da irin wannan bilumbituwar da Okorocha ya rika yi daga wannan jam’iyya zuwa waccan, ya rike AA, bai kyale ta ta mutu murus ba.

Yayin da APC ta ki tsayar da surikin sa Uche Nwosutakarar gwamna, sai ya koma AA, inda aka tsaida shi dan takarar gwamna.

Wannan gwasalewar da aka yi Okorocha ce ta hada shi rikici da shugabannin APC na kasa baki daya, ciki har da uban jam’iyya, Bola Tinubu da Adams Oshiomhole.

Tun su na sheka wa juna bakaken maganganu, sai da ta kai su ga goranta wa juna da kuma surfa wa ashariya.

Wannan bai sa Okorocha ficewa daga APC ba, domin a yanzu ma shi ne dan takarar sanata na yankin su, tunda a wannan zaben ne wa’adin sa na gwamnan shekara takwas zai cika.

OKOROCHA: KARO DA GOMA SAI SHIRYAYYE

Ranar Asabar da ta gabata an kwashi ‘yan kallon kwatagwangwama tsakanin Okorocha da matar Mataimakin Shugaban Kasa, wadda ta wakilci uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari a taron matan APC a jihar Imo.

Okorocha ya shiga cikin taron matan tsamo-tsamo ya ce kada su zabi dan takarar APC, su zabi Nwosu, dan takarar AA.

Wannan furuci kuwa Okorocha ya yi shi ne a gaban Hope Uzodimma, dan takarar gwamnan APC.

Okorocha ya ce babu abin da zai hana Nwosu zama gwamna kuma shi za a rantsar a ranar 29 Ga Mayu.
Sai dai kuma ya ce Buhari za su zaba a matsayin shugaban kasa.

Amma kuma a jiya Litinin shugaban jam’iyyar AA, ya ce Atiku za su zaba, ba Buhari ba.

Share.

game da Author