Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa za a fara atisayin ‘Operation Python Dance’ a Maiduguri jihar Barno.
Jami’in rundunar Abdulmalik Biu ya sanar da haka a taron kadamar da atisayin inda ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya ta shigo da wannan atisayin a shekaran 2018 a kasar nan domin kama masu aikata miyagun aiyukka.
Ya ce rundunar za ta fara atisayin ne daga yanzu zuwa ranar 28 ga watan Faburairu.
” Wannan atisayi ana yin sa ne domin samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin mutane musamman a yanzu da zaben 2019 ya tunkaro.
Sannan muna gargadin matasan da ke aikata ayyukan ta’addanci da su kwana da shirin kuka da kan sa domin sai ya dandana kudar sa.