Mahara sun kashe mutane 26 a garin Gandi da ke Gundumar Karamar Hukumar Rabah ta Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce an kai mummunan harin ne jiya Litinin da dare a kauyukan Warwana, Tabkin Kwasa da kuma Dutsi, inda suka rika yin harbin kai mai uwa da wabi.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Murtala Mani ya tabbatar da wannan hari.
Mani ya shaida wa manema labarai cewa an kara kai jami’an tsaro a yankin domin taimaka wa wadanda ke can a kamo maharan da suka yi kisan.
An ce dukkan su a kan Babura suka kai harin.
Dama a cikin watan Yuli na shekarar da ta gabata sai da aka kai wa garin hari aka kashe mutane da yawa.
An kona kauyuka da dama a wancan hari na watan Yuli da aka kai.
Sarkin Goronyo Muhammadu Aliyu ya ce muatane da ya yawa sun gudu sun bar kauyukan.
Ya ce wadanda suka kai wannan harin ba irin wadanda suka kai wancan harin na baya ba ne. kuma ba irin masu zuwa suna satar shanu ba ne.
Ya kara da cewa an kama akalla mutane 70 a cikin kauyuka 17 na yankin Goronyo a cikin shekaru biyu. Kuma na biya diyyar da ta kai naira miliyan 100.
Gwamna Aminu Tambuwal ya katse kamfen da ya ke yi a Goronyo, ya shaida wa mutane labarin kai harin, sannan kuma ya nemi a yi addu’a.