Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa jihohin Sokoto da Jigawa ta’aziyar rasuwar magoya bayan jam’iyyar APC da aka yi a cikin wannan makon nan.
Shehu ya isar da sakon ta’aziyar da Buhari wa jihohin ne ranar Alhamis.
Ya ce jam’iyyar ta rasa rayukan magoya bayan ta hudu a jihar Jigawa a dalilin hadarin mota suka yi ranar Litini.
” A ranar Litini wasu magoya bayan jam’iyyar APC guda goma sun yi hadarin mota a hanyar su na zuwa taron gangamin jam’iyyar da aka yi a jihar. hudu daga cikin su sun rasu sannan sauran sun sami raunuka.
Bayan haka Shehu ya kuma ce jam’iyyar ta sake rasa rayukan wasu magoya bayan ta biyu a jihar Sokoto ranar Laraba a dalilin turmutsutsu da aka yi a filin taron Jam’iyyar.