ABUJA: Mutanen Dutsen Alhaji sun yaba samar musu da wutan lantarki mai amfani da hasken rana

0

Ranar Alhamis din da ya gabata ne aka kadamar da na’urar samar da wutan lantarki da hasken rana wato Sola a cibiyar kiwon lafiya dake Dutsen Alhaji Abuja.

Kamfanin ‘PVWater International Ltd’ da ma’aikatar kiwon lafiya ne suka hada hannu wajen yin wannan aiki.

Bayanai sun nuna cewa na’urar zai samar da ruwa da ya kai lita 20 duk rana.

Wata mazauniyar wannan unguwa mai suna Madam Popular ta bayyana cewa samar musu da wannan na’ura zai taimaka musu matuka wajen wadata su da wutan lantarki da suke fama da shi tun-tuni a unguwar.

Ita kuwa Adeniyi Mary cewa ta yi sauki suka samu musamman wajen siyan ruwa da suke yi. Yanzu wannan inji zai samar musu da ruwan sha yadda ya kamata ba sai sun yi ta kashe kudi ba suna siyan ruwa. ta ce yanzu aikin yi ya rage gwamnati ta samar wa matasan jihar.

Da yake kaddamar da na’urar karamin ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa samar da ruwa da wutan lantarki na cikin mahimman ababen inganta rayuwa musamman wanda ya shafi fannin kiwon lafiya.

Daga nan kuma jami’in kamfanin PVWater Anthony Ighodaro ya mika godiyarsa bisa yadda gwamnati basu hadin kai da goyon baya har aka samu nasarar kammala wannnan aiki.

A karshe dakacen Dutsen Alhaji Abubakar Bako ya jinjina aiyukkan da gwamnati da kamfanin PVWater suka yi musu sannan ya kuma yi kira ga mutanen yankin da su dinga yin kokari biyan Naira biyar ga kowace litar ruwa da za su diba a wurin.

Share.

game da Author