ZABE: An kama hadimin Gwamnan Jigawa ya na kekketa fastar ‘yan Adawa

0

Dan takarar jam’iyyar SDP a Jihar Jigawa Bashir Adamu, ya yi korafin cewa hadimin Gwamna Mohammed Badaru, mai suna Bala Idi ya rika bi ya na kekketa fastocin ‘yan adawa a garin Kazaure.

Hakan ta faru ne a lokacin da ake shirye-shiryen zuwan Gwamna Badaru kamfen a Kazaure.

Bala Idi shi ne mashawarcin gwamna a kan hakokin mu’amala da sauran jam’iyyun adawa a jihar.

Bashir Adamu wanda shi ne dan takarar SDP a jihar Jigawa, ya shaida wa manema labarai cewa hadimin ya ja zugar matasa ‘yan ta-kife sun rika kakkarya allunan da ke dauke da fastoci da kuma kekketa hotuna da balle fastocin da lika jikin bango da bishiyoyi.

Wani hoto da PREMIUM TIMES ta samu, ya nuna Idi ya na kece wata fastar dan takarar gwamnan SDP a garin Kazaure.

Badaru ya yi kamfen ne a yankin Kazaure da ‘Yankwashi a karkashin jam’iyyar APC.

Adamu ya yi ikirarin cewa matasa ‘yan ta-kifi sun rika kai wa masu adawa hari a garin.

Adamu shi ne tsohon dan majalisar tarayya na Kazaure, Yankwashi, Roni da Guiwa.

Ya yaba wa Kwamishinan ‘yan sandan jihar ganin yadda ya saurari korafin sa ba tare da ya goyi bayan kowane bangare ba.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Abdul Jinjiri ya tabbatar da cewa Adamu ya shigar da korafin a hannun su. Kuma za su yi bincike su dauki matakin da ya dace.

Share.

game da Author