Ba a nada Dangote a Kamfen din Buhari ba, na shi fagen shawara ne – Fadar Gwamnati

0

Babban mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana cewa ambatar sunan Hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote a cikin jerin kwamitocin kamfen din Buhari cewa ba a saka shi ba don yayi wa Buhari Kamfen bane.

” A matsayin Dangote na wakili a kungiyar zaman lafiya sannan kuma shi ba dan jam’iyyar APC bane domin ko katin zama dan jam’iyyar bai mallaka ba babu yadda za a ce zai kasannce mai yi wa Buhari kamfen.

Jam’iyyar PDP ta koka kan saka sunan Dangote a jerin sunayen mabobin kwamitocin da za su rika shirya wa Buhari tarorrukan Kamfen.

Ta ce a matsayin sa na dan kasuwa sannan hamshakin attajiri Buhari na yi musu shigo-shigo ba zurfi ne, ” Idan suka shigo Kamfen din sa suka kashe kudaden su sai bayan ya ci zabe sai ya kame su duka ya daure su cewa sun kashe kudaden da bai kamata. Saboda haka ina kira a gare su musamman Dangote da Otedola da sunayen su ke ciki da su rika sara suna duban bakin gatarin su, kada su fada cikin tarkon Buhari.

Kassim Afuegbu da ya bayyana haka a madadin PDP ya ce maimakon a saka sunayen Otedola da Dangote ciki kwamitin tsara tattalin Arzikin kasa ne sai awani saka su cikin kwamitin kamfen.

Share.

game da Author