Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ritsa Sanata Dino melaye a gidan sa, a bisa umarnin a kama shi, saboda ya jagoranci an ci zarafin wani jami’in dan sanda.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labaran ‘Yan sanda na Kasa, Jimoh Moshood ya bayar, ya ce Dino Melaye ya ja zugar wasu masu ‘dauke da makami’ suka harbi wani Saje Danjuma Saliu a cikin watan Yuli.
Kafin nan sai da PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa ‘yan sanda sun kewaye gidan Dino Melaye, kuma sun yi dandazo a kan titin da ya nufi gidan sa, a cikin unguwar Maitama, Abuja.
Jimoh ya ce an harbi Saje Danjuma Saliu ne a kan hanyar Aiyetoro, Mopa, cikin jihar Kogi a lokacin da ya tsaida su Dino da tawagar sa a kan titi domin ya bincike su.
Danjuma, wanda dan sandan Mobal ne, an ce an harbe shi a ranar 18 Ga Yuli, 2018.
“Har yanzu dan sandan bai gama warkewa daga harbin bindigar da aka yi masa ba, saboda raunin da ya ji ya yi tsanani sosai.” Inji bayanin da Moshood ya fitar jiya Juma’a.
Bayan nan kuma ‘yan sanda sun ce sun aika da wasikar sanarwa ga Magatakardar Majalisar Tarayya kamar yadda doka ta tanadar tunda Dino Sanata ne.
Haka kuma jami’an sun ce Dino ya na cikin gidan, ba kamar yadda ya yi karyar cewa ba ya gidan ba.
A shekaranjiya Alhamis ne Dino ya bayyana cewa ‘yan sanda na kokarin kama shi, inda nan take su kuma suka ce karya ya ke yi musu, babu wani shiri na kama shi da suke yi.
Kwana daya bayan wannan jawabi da ‘yan sanda suka fitar, sai aka wayi gari kuma jami’an su sun yi wa gidan sa zobe a cikin unguwar Maitama, Abuja.
Sun ce ba za su bar gidan ba har sai ya fito sun kama shi.
Discussion about this post