Fadar shugaban kasa ta fada cikin rudani game da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan jihar Zamfara.
Ga dukkan alamu rudewar ya kai ga gwamnati ba ta san ko inane aka kashe mutane a jihar ba kamar yadda ya nuna a sakon jajentawa mutanen jihar da ya fito daga fadar shugaban kasa.
A wannan sako dai idan ba a manta ba wanda Garba Shehu ya saka wa hannu, Buhari ya ce ya na jajentawa mutanen garin Birnin Magaji da ke karamar Hukumar Tsafe da mutanen kauyen Magami dake gundumar Faru, Karamar Hukumar Maradun bisa harin da ‘yan ta’adda suka kai musu da yayi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.
Sai dai kuma ko a rashin sani ko kuma ganganci za a iya cewa hakan na nuni da cewa shugaban kasan bai san yadda tsarin jihar Zamfara yake ba da inda ake kaiwa mutane hare-hare domin garin Birnin Magaji ba a cikin karamar hukumar Tsafe take ba. Ita kanta karamar hukuma ce mai cin gashin kanta. Sannan Birnin Magaji din ce hedikwatar karamar hukumar.
Wasu da suka tofa albarkacin bakin su game da wannan ganganci da fadar gwamnati tayi sun yi tir da hakan inda suka ce hakan na nuna da cewa shugaba Buhari ma bai san takamammen garin da aka kai wadannan hare-hare ba.
” Babu ta inda Buhari zai iya tsame kan sa daga wannan katobara da gwamnati ta yi. Hakan na nuni da cewa akwai rashin natsuwa da fahimtar halin da mutanen kasa ke ciki daga bangaren shugaban kasa da za a ce wai Buhari bai san cewa Birnin Magaji ba cikin karamar Hukumar Tsafe ta ke ba, cewa ita kanta karamar Hukuma ce mai zaman kanta.” Haka Sola Olubanjo ya fadi.