DALLA-DALLA: Yadda INEC za ta gudanar da zaben 2019

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana tsarin da za ta bi wajen gudanar da zabukan 2019.

Kwamishinan Tarayya na INEC, Festus Okoye ne ya furta haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a wurin wani taron sanin-makamar-aiki a Abuja.

Okoye, wanda kuma shi ne Shugaban Wayar da Kan Masu Kada Kuri’a, ya kara yin bayani dangane ne tambayoyin manema labarai a kan yadda za a rika dauko labaran yadda zabuka ke tafiya da kuma bayyana sakamako.

1 – Sai wanda ya yi rajista kuma ya na dauke da katin shaidar rajista na dindindin, wato PVC zai yi zabe, bayan na’urar CARD Reader ta tantace shi.

2 – Kowane mai kada kuri’a zai jefa kuri’ar sa da kan sa, babu aike, kuma babu wakilci, babu dan rakiya. Kamar dai yadda INEC ta gindaya sharudda.

2a – INEC ta dauki ma’aikatan ta da kuma ma’aikata na wucin-gadi da za su gudanar da zabe.

3 – Wadanda aka amince su tsaya a rumfar zabe sun hada Jami’an INEC da ke aiki a rumfar, jami’an tsaro, ‘yan takara ko ejan din su, ‘yan jaridar da aka tantance, aka ba su izni da kuma masu sa-ido na cikin gida da baki na kasashen waje.

4 – Za a fara tantancewa da na’urar ‘Card Reader’, sai duba sunaye a cikin rajista, dangwala wa yatsa tawwada. Za a yi kokarin tantance yatsan mai zabe a na’ura sau hudu.

5 – Idan na’ura ta kasa tantance mai zabe, sai a nusar da babban jami’in zabe, wanda zai tsaya ya duba, idan ya gamsu cewa rajistar sunan sa ne, kuma ya gamsu ba a tantance shi a wani ya je ya yi zabe ba, to shikenan.

6 – Za a kyale wakilan gidajen jaridu da masu sa-ido su shiga rumfunan zabe, dakunan tattara bayanai da kuma wuraren raba kayan zabe.

7 – Ba a yarda a karya dokar zabe ta hanyar yin rakodin na yadda wani mai kada kuri’a ya jefa ta sa kuri’ar ba.

8 – An amince wa kafafen yada labarai su yi rakodin ko amfani da sakamakon yawan kuri’un da kowane dan takara ya samu idan har INEC ta fito da su a takardar da ta ke lika sakamako EC60(E).

9 – Ba a yarda ba kafafen yada labarai ko masu sa-ido su bayyana sakamakon zabe, domin ba aikin su ba ne, aikin babban jami’ain zaben da ke da alhakin bayyanawar ne.

10 – Doka ta 123(4) ta Dokokin Zabe ta shekarar 2010 ta ce duk wanda ya yi gangancin bayyana sakamakon zabe, domin ya san yin hakan karya ce ya kitsa, ko kuma ya saba wa sakamakon da INEC ta fitar, to zai fuskanci daurin shekaru uku, wato watannin 36.

Share.

game da Author