A cikin wani bidiyo da aka fallasa, Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya bayyana babban dalilin batawar sa da kuma haushin da ya ke ji wa Shugaba Muhammadu Buhari, cewa ya samo asali ne daga rashin gudanar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ba ta yi ba jihar Kwara, duk kuwa da dimbin gudummawar makudan kudaden da ya bai wa tafiyar kamfen din Buhari a yakin neman zaben 2015.
Saraki kuma ya yi ikirarin cewa a lokacin yakin neman zaben Buhari a 2015, ya kashe kudi kusan naira bilyan daya a jihohi 30 daga cikin jihohi 36 na kasar nan, duk domin kamfen din Buhari.
Da ya ke jawabi a gaban wasu ‘yan jam’iyyar sa a jihar Kwara, Saraki ya ce gwamnatin tarayya ba ta da niyyar tsinana wa jihar Kwara da jama’ar ta komai. Ya ce da an bai wa ‘yan jihar mukamai kamar yadda aka fifita wasu bangarori, to da al’ummar jihar ba su shiga cikin kunci kamar yadda suke ciki a yanzu ba.
Maganganun da Saraki ya yi da harshen Yarbanci ya yi maganar ta tsawon minti 33, ga wasu magoya bayan PDP na jihar.
Tuni dai aka rika yada wannan kalami na sa a a soshiyal midiya.
Wani mai suna Kayode Ogundamisi ne ya fara watsa shi a shafin sa na twiter.
“Yayin da na bar PDP na koma APC, na sadaukar da kai na ina yi wa APC kamfen irin yadda ban ma taba yin kamfen a baya ba. Na yi rangadi jiha-jiha ina taya Buhari kamfen har lokacin da aka yi zaben 2015.
“Daga cikin jihohi 36 na kasar nan, na biya domin gudanar da harkokin zabe na jam’iyya har a cikin jihohi 30. Na raba naira milyan 400 a wasu jihohi, wasu milyan 300, wasu kuma naira milyan 200.
A jihohin Kudu maso Yamma ne kadai ban raba kudade ga kamfen din Buhari ba.
“Sai da ta kai ni har da baki na ke bai wa manajojin banki umarnin a fitar da kudade . Tunanin mu a lokacin idan an yi nasara za a aka wa mutane na da manyan mukamai, kamar yadda aka rika saka wa wasu mutanen wani yankin.
“Ku kan ku na sha fada muku a lokacin kamfen cewa idan ranar rantsuwa ta zo, tare ma za mu tafi Abuja, domin ina sa ran za a ba ku manyan mukamai irin su hukumomin FERMA, NITDA, NPA ko UBEC da sauran su.”
Saraki ya yi korafin yadda a karon farko a kasar nan, bayan zaben 2015, Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Tarayya ba su iya sawa a dauki ko da mai shara aiki ko su dauka da kan su.
Yayin da jama’a da dama ke bayyana damuwar su a kan bidiyon, da dama na cewa Saraki ya fadi abin da ke cikin zukatan jama’ar kasar nan da dama, musamman daruruwan wadanda suka taimaka wa Buhari da makudan kudade, amma ya watsar da su ko ya yi musu butulci.
Sai kuma ofishin Saraki ya maida martani a kan muryar da aka ce ta Saraki din ce.
Kakakin Yada Labarai ya ce masu adawa ne ke neman ko ta yaya sai sun kauda Saraki, kuma hakar su ba za ta cimma ruwa ba. Ya ce duk abin kirkira ce, ba gaskiya ba ne.