2019: Buhari zai kaddamar da kamfen a Abuja

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da kamfen din takarar shugabancin Najeriya a karo na biyu yau lahadi a dakin taro dake fadar shugaban kasa.

Idan ba a manta ba hukumar zabe ta dage dokar hana gudanar da kamfen ne daga Asabar 18 ga watan Nuwamba.

A taron gaddamar da kamfen din tazarce na shugaba Buhari ana sa ran gaggan ya’yan jam’iyyar APC duk za su halarci wannan taro.

Ministan makamashi da Ayyuka, Tunde Fashola ne zai bude fili da yin bayanai kan ayyukan da gwamnati ta ke yi tun bayan darewa karagar mulki a 2015.

Sannan kuma ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya dora daga inda Fashola zai tsaya.

Ministan Kudi za ta yi bayani kan irin kokarin da gwamnatin Buhari ta yi duk da karancin kudaden shiga da take samu tun daga 2015 zuwa 2018.

Minstan Ayyukan Gona, Audu Ogbe da Maryam Uwais duk za su bayani kan ci gaban da aka samu zuwa yanzu a kasar nan.

Bayan haka za a nuna bidiyo har guda hudu domin nuna irin ayyukan da gwamnati ta yi kuru-kuru ba a takarda ba kawai domin kowa ya shaida ba hira bace ko boge, yadda aka fadi haka aka yi.

Babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar zai Kaddamar da na sa Kamfen din ranar Litini amma a shafin sa na Facebook.

Share.

game da Author