Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya ce babu hannun sa a cikin gayyatar da jami’an SSS suka yinwa Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole, inda ya shafe kusan yini daya ana sheka masa ruwan tambayoyi.
An ruwaito cewa Oshiomhole ya sha tambayoyi ne a ranar Lahadin da ta gabata, dangane da rubutaccen kofare-korafe da wasu gwamnanonin APC suka gabatar cewa shugaban na jam’iyyar APC ya kakkarbi kudaden toshiyar baki a lokacin da ake ta hada-hadar gudanar da zabukan fidda gwani na ‘yan takarar APC a fadin kasar nan.
Gwamna Amosun na daya daga cikin masu rikici da Oshiomhole, tun bayan da dan takarar da ya ke so ya gaje shi, Adekunle Akinlade ya sha kaye a hannun Dapo Abiodun.
Sauran gwamnonin da ke rikici da Oshimhole sun hada da Rochas Okorocha na Imo da Abdulziz Yari na Zamfara.
Da ya ke magana da manema labarai bayan sun fito daga wani taron gaggawa da Shugaba Muhammadu Buahari, Amosun ya jaddada cewa ai a matsayin sa na gwamna ba shi da karfin ikon da zai sa SSS su binciki Oshiomhole, Shugaban jam’iyyar APC.
“Wannan tambaya da ku ka yi min kamar kun a dora min wani ikon da ban i da shi ne. Kun ga dai ni ba jami’in tsaro ba ne. Don haka ina ganin kamar dai wannan tambayar ba ni ne za ku yi wa ita ba.”inji Amosun.
“Ni idan fada zan yi da Oshiomhole, ai ni da shi za mu-yi-ta-ta-kare, ba sai na dauki sojojin haya ba. Ku ma kun san haka, kuma kun san ni da kyau.”
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Oshimhole ya arce kasar Amurka, inda aka rika yada jita-jitar cewa ya tsere ne, domin zafin wutar da ce bugar masa fuska ya lafa tukunna, kafin ya dawo.