Kakakin hukumar kurkukun Najeriya (NPS) Chukwuemeka Monday ya bayyana cewa bana furzinoni 129 ne suka yi rajista da Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa, NECO don yin jarabawar NECO a bana.
Monday ya fadi haka ne a garin Enugu da yake ganawa da manema labarai.
Jami’in hukumar Ibrahim Usman ya bayyana cewa an dade ana koyar da wadannan furzinoni darussan da za su rubuta kafin yanzu.
Ya ce adadin yawan wadanda za su rubuta jarabawar a bana sun fi na bara.
Discussion about this post