INEC ta bayyana sunayen jam’iyyun da za su shiga zaben fidda-gwani a Katsina, Bauchi da Cross-River

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana sunayen jam’iyyun da za su fatata takarar zaben cike-gurbin dan majalisar tarayya mai wakiltar wasu yankuna a jihohin Bauchi, Katsina da Cross River.

Za a gudanar da zabukan cike gurabun ne a ranar 17 Ga nuwamba.

Hukumar ta ce jam’iyyun da suka gabagar da sunayen ‘yan takarar su, sun hada PDP, PRP, YES, APC, LP, UPN da kuma PPN.

Wannan sanarwa na kunshe a cikin wata takardar manema labarai da Kwamishinan Zabe na Kasa, mai kula da kwamitin yada labarai da ilmantarwa kan batutuwan da suka shafi zabe ya fitar a jiya Alhamis.

Ya kuma jaddada cewa an yi dukkan shirye-shiryen da za a tabbatar da cewa an samu gagarimar nasarar gudanar da sahihin zabe ba tare da tashin hanli ba.

A katsina za yi zaben cike gurbi a mazabar Kankia/Kusada/Ingawa. A Bauchi kuma za a yi zabe a Karamar Hukumar Toro. A jihar Kwara za a yi zabe a mazabar Ekiti/Irepodum/Isin/Oke-Ero sai kuma a jihar Cross Rivers za a yi zaben cike gurbi a Ikom II.

A jihar Katsina, PRP, YES, PDP da APC ne za su shiga takara. A Bauchi kuma APC da PDP ne kadai. A Kwara akwai LP, UPN, PDP, PPA. A Cross River kuwa, jam’iyyar PDP ce kadai ba ta da wata mai hamayya.

Share.

game da Author