SHEHU SANI: Tsira Da Mutunci Ko Batan-bakatantan?

0

Daga jiya Talata, 23 Ga Oktoba dai ta tabbata cewa Sanata Shehu Sanin a Jam’iyyar APC mai wakiltar Shiyyar Kaduna ta Tsakiya, ya jefar ko kuma ya kekkketa katin shaidar sa na dan jam’iyyar APC, zuwa PRP.

Ba a yi mamakin canja shekar da ya yi ba, sai ma mamakin yadda ya yi sakaci da jinkiri har sai da ta kai yanzu sannan ya fice daga APC.

Sani na daya daga cikin wadanda suka yi fafutikar kafa gwamnatin APC, inda ya nemi takarar sanata, kuma ya yi nasara.

Sai dai kuma tun ba a dade da kafa gwamnati ba, sai aka fara samun takun-saka tsakanin Sani da gwamnan Kaduna da ya yi nasara a karkashin APC shi ma, wato Nasir El-Rufai.

Wasu na ganin cewa sabanin ya fara samun asali ne, tun bayan da gwamna ya wancakalar da sunayen na hannun damar siyasar Sani da shi sanatan ya nemi a ba su mukamai a cikin gwamnatin jihar Kaduna.

Amma wasu kuma na ganin cewa sabanin ba ya rasa nasaba da neman shishshigi da ba-ni-na-iya da aka ce Sani ya nemi ya rika yi wa El-Rufai a gwamnatin sa, ko kuma sha’anin tafiyar da mulkin sa.

Sabanin da ke tsakanin su ya na kan turbar siyasa, har ya kai rikida, ya zama gaba tuburan muraran a tsakanin sanatan da kuma gwamnan.

Shehu Sani ya rika fitowa a kafafen yada labarai ya na sukar manufofi da alkiblar gwamnatin El-Rufai. Shi kuma gwamnan da ya ke za ni ce, ta taras da mu je, sai ya daura banten kokawa da sanatan kama a kafafen yada labarai har tsakiyar bainar jama’a a wurin taruka.

Ba a nan su ka tsaya ba, sai da tirka-tirkar kokawa ta mirgina su har cikin kotu.

SHEHU SANI: RAINA KAMA KA GA GAYYA

Babban abin da Shehu Sani da sauran sanatocin jihar Kaduna uku suka yi wa El-Rufai wanda ya fi harzuka da su, shi ne kin amincewar da suka yi a Majalisar Dattawa Jihar Kaduna ta karbo bashin dalar Amurka sama da milyan 300.

Wannan ya fusata gwamnan matuka gaya, inda shi kuma ya rika yi musu jifar kan-mai-uwa-da-wabi.

Daga wanda ya maka kotu, sai wanda ya ruguje wa gida, sai kuma jam’un tsinuwa da yay i musu gaba dayan su ukun. Sai kuma Shehu Sani da aka tafka kakudubar hana shi sake fitowa takarar sanata karo na biyu, aka ba dan gaban goshin El-Rufai, Uba Sani.

El-RUFAI: WUKAR YANKAN GIWA…

El-Rufai ya nuna wa Sani cewa wukar yanka fatar giwa fa ba girma ake nema ba, sai dai kaifi. Duk da taron dangin da sauran jiga-jigan siyasar APC na Kaduna, irin su Sanata Hunkuyi da sauran sanatocin suka yi wa El-Rufai, hakan bai sa sun kai shi kasa har keyar sa ta dunguri turbaya ba.

Shi da kan sa ya taba mikewa tsaye a cikin jama’a ya ce duk wanda ya yi karo da shi ba zai iya cin nasara a kan sa ba.

Gwamnan ya dauki rikigimar da zafi sosai, har ta kai kusan a kasar nan, jihar Kaduna ce aka fi tafka rikita-rikitar hayaniyar siyasa a cikin jam’iyyar APC.

Rashin girman jiki na El-Rufai ba ta hana shi yin nasara a kan kowane abokin rigimar siyasar ba. Ya nuna musu cewa shi fa ruwan aski ne, wanda ba shi da yawa, amma akwai sa gashi laushi.

SANI: MAI RABON SHAN DUKA

Rikicin siyasar da ya dabaibaye jam’iyyar APC ya sa sauran sanatocin jihar Kaduna ficewa daga jam’iyyar a watannin da suka gabata. Kowa a kasar nan ya yi tsammani Shehu Sani zai kasance na farkon ficewa daga jam’iyyar, ko dai saboda rikicin da ya ke tafkawa da gwamna El-Rufai, ko kuma saboda yawan sukar da ya ke wa APC, ya na cewa ta saki layi da turbar da aka kafa ta, saboda son ran shugabannin jam’iyyar da kuma wasu ‘yan tsirarun gwamnoni, da kuma wasu fadawan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sani bai fice ba, ya tsaya neman kamun-kafa ga Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole, wanda suka yi gwagwarmayar kungiyoyin kwatar hakki tare a can baya. Ya kuma rika yin rara-gefe a jikin Buhari har zuwa lokacin zaben fidda-gwani, wanda a karshe dai jam’iyya ta ki tabbatar da shi, ta tabbatar da yaron gwamna El-Rufai, a matsayin dan takarar sanata na zaben 2019, ba Shehu Sani ba.

TAMBALEBALE KO BATAN-BAKATANTAN?

Tambayar da mutane ke ta yi bayan Shehu Sani ya rasa tikitin takara, me ya hana shi bin abokan gwagwarmayar rikici da APC, irin su Sanata Dino Melaye, Bukola Saraki da Yakubu Dogara ba? Tsoron me ya ke ji.

Yanzu kuma da ya fice daga APC, bayan jam’iyyar ta tozarta shi, shin wane tasiri zai iya yi a jam’iyyar PRP da ya koma? Shin magoya bayan sa, ‘yan akidar jam’iyyar PRP ce ta ainihi, da za su bi shi duk cikin surkukin jeji ko kogon dutse da gwazazzabon siyasar da ya ja su ya kai su? Ko kuwa za su tarwatse ne su rabu da shi, kowa ya kama mai hannu da shuni, wanda Hausawa ke cewa shi ake ba murjin zare?

PRP: A DAURI KASHI KO A BATA IGIYA

A Arewa dai jam’iyya biyu ce kadai ke da tasiri, wato APC da PDP. Zai yi wahala wata jam’iyya daga cikin jam’iyyu 91 da suka yi rajista ta yi wani hobbasa a zaben 2019.

Su kan su masu zabe sun karkata hankulan su a kan APC da PDP kadai. Sannan kuma akasarin masu komawa PDP a Kano da Kaduna, duk hasalallun da aka tarwatsa wa lissafi ne daga APC ko PDP.

PRP ba ta da karfin yin gwagwagwar kamfen da kuma tirka-tirkar wadata wakilan ta a dukkan rumfunan zabe a ranar zaben sanatoci, wanda a wannan ranar kowa hankalin sa zai fikarkata ne ga APC ko PDP.

RABON KWADO BA YA HAWA SAMA

Duk da wannan hasashen siyasa da ake yi, zai iya kasancewa Shehu Sani ya kai ga yin nasara, musamman ganin yadda rigingimu suka dabaibaye jam’iyyar APC a jihohi da dama a Arewa da kudancin kasar nan.

Matsawar masu goyon bayan Sanata Shehu Sani suka yi kumumuwa, suka bi shi duk inda ya jefa kafar sa, sannan kuma sauran hasalallun da APC ba ta kyauta musu ba tun daga zaben shugabannin kananan hukumomi, na jihohi har zuwa na matakin shugabannin jam’iyya na kasa, da kuma wadanda ba a kyauta wa ba a zabukan fidda-gwani, to Shehu zai iya sake hawa kan kujerar sa.

Saura da me, ko El-Rufai zai bar shi ya kai labari? Shin APC za ta yi wa El-Rufai tazarce a Kaduna?

Ko shakka babu, idan har su biyun kowa ya koma kan kujerar sa, to daga 2019 har zuwa 2013 za su ci gaba da kwasar ‘yan kallo, domin ba mamaki wata rana a ga musu gangar kokawa na buga wa kowa kirarin sa a tsakiyar tashar Kawo, Kaduna.

Shehu dai ya ce ya fice daga APC domin babu sauran masu mutunci a cikin jam’iyyar. Shin ko shi ma ya na da mutuncin da magoya bayan PRP za su mutunta shi, yadda ba za su bari zanin sa ya kwance a gaban El-Rufai ba?

Kada fa Shehu ya yi abin da Bamaguje ke kira ‘tambale-bale’, wai mutuwar almuru – mutum ya mutu kafin a gama tuwon dare a duniya, a lokacin da za a gama yi masa kuka har a bizne shi, dare ya yi, har na lahira sun gama cinye na su tuwon.

Akwai kallo a ranar zabe.

Share.

game da Author