Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu ya karyata jita-jita da kuma labaran da wasu kafafen sadarwa suka watsa cewa zai fice daga jam’iyyar PDP.
Ekweremadu wanda yanzu haka ba ya cikin kasar nan, ya fito yau Laraba da safe ya bayyana a shafin sa na Facebook cewa har yanzu ya na cikin PDP kuma bai ce zai fita ba.
Ya ce shi makomar siyasar a hannun ubangijin sa ta ke, don haka ya na kara godiya da dama da kuma tasirin da ya ba shi a siyasa.
Ekweremadu ya kara da cewa shi alkiblar siyasar sa tafiya ce mai tasirin gina dimokradiyya ta hanyar tafiya tare da sauran dukkan bangarori na jama’a, kowane yanki, kowace kabila ta sani kuma ta gani cewa ana damawa da ita.
Daga nan sai ya gode wa iyalan sa, abokai, abokan siyasa da kuma sauran wadanda suka rika kiran sa domin jin gaskiyar komawar sa APC ko a’a.
Ya ce shi a yanzu ba shi da wata damuwa, musamman ma ganin irin dimbin magoya baya da ya ke da su a fadin kasar nan.
“Ina kara jaddada muku cewa ina nan daram a PDP.” Inji shi.
An rika yada cewa Ekweremadu zai koma APC saboda haushin dan takarar jam’iyyar PDP na zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dauki mataimakin takarar sa daga yankin Ekweremadu, ba tare da an tuntube shi ba.
Akwai zargi mai karfi kuma cewa shi ma Ekweremadu din ya nemi Atiku ya tsaida shi mataimaki, amma bai yi haka din ba, sai ya dauki Peter Obi.