Mai Shari’a Mojisola Olatoregun da ke Babbar Kotun Tarayya a Lagos, ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose.
An bayar da belin na sa ne safiyar yau Laraba a kan sai an ajiye kudi naira milyan 50 da kuma masu karbar beli biyu da kowanen su ke da shaidar takardar biyan haraji ta shekaru uku da suka gabata a jere.
Ta kuma umarci Fayose ya ajiye fasfo din sa na fita kasashen waje a kotun.
Tun da farko, lauyan Fayose, Kanu Igabi ya roki kotu ta bayar da belin Fayose a bisa dalilin cewa shi da kan sa ne ya kan sa a ofishin EFCC, ba kama shi aka yi aka kai shi ba.
Sai dai kuma jami’an EFCC ba su yard aba bayar da belin sa ba, saboda a cewar su, lokacin da Fayose ya kai kan sa EFCC, ya isa tare da rakiyar gungun batagarin da suka nemi kai wa jami’an na su farmaki.
Hukumar ta kara da cewa har yanzu su na ci gaba da binkicen sauran kadarorin da Fayose ya mallaka da ya saya daga cikin kudaden da aka yi zargin ya wawure.
.
Ana tuhumar Fayose da kamfanin sa mai suna Spotless Limited da laifuka 11, wadanda idan aka tattara kudaden da ake nema a wurin sa, za su kai naiara bilyan 2.2. Ya shaida wa kotu cewa bai aikata ko daya daga cikin laifukan da ake tuhumar sa ba.